1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Faɗa ya sake ɓarkewa a jihar Plateau.

Halimatu AbbasJuly 17, 2010

Mutane takwas sun rasa rayukansu a wani sabon rikici a jihar Plateau da ke Najeriya.

https://p.dw.com/p/OO6Z
Wani gida da aka lalata a rikicin Jos.Hoto: AP

 A jihar Plateau ta Tarayyar Najeriya, wasu mutane ɗauke da makamai sun kai hari akan iyalin wani limamin coci tare da cunna wa cocinsa wuta. Wannan artabun ya faru ne a daidai kusa da inda wasu ɗaruruwan mutane suka rasa rayukansu yayin wani tashin hankali da ya ɓarke a wannan shekara. Mazauna wannan wuri sun ce da sanyin safiyar yau Asabar ne wasu da ba a san ko su wa nene ba, suka kai hari akan iyalin Rev. Nuhu Dawat a ƙauyen Maza da ke da tazarar kilomita 12 daga Jos babban birnin jihar, suka kashe matansa da 'ya'yansa biyu da kuma jikansa.  Rev Dawat wanda shi ne kaɗai ya tsira daga cikin iyalin nasa ya gudu ne a lokacin wannan hari. A baya ga iyalin limamin coci an kuma samu wasu mutane huɗu da suka rasa rayukansu. 

Mawallafiya: Halima Balaraba Abbas

Edita: Yahouza Sadissou Madobi