Fada ta barke a Guinee
November 15, 2010Talla
An bada rahoton cewa fada ta barke tsakanin jam'ian tsaro da da wasu daruruwan matasa a Conakry Babban birnin kasar Guinee, a dadai lokacin da ake cikin zaman jiran hukumar zabe ta kasar ta bayyana sakamakon zaben na shugaban kasar da aka gudanar a makon jiya.
Wani babban jam'in yan sanda da ya ce sun tarwatsa matasan galibi magoya bayan tsohon Firaminista Cellou Dalein Diallo,
ya ce suna kokarin tayar da fitinan ne a wata cibiyar ta yan siyasar a sa'ilin da suka fatatakesu.Nan da wani lokaci ne dai a yau aka shirya hukumar zaben za ta bayyana dan taraka da yayi nasara a zaben shugaban kasar zagaye na biyu tsakanin Alpha Conde da Mista Diallo.
Mawallafi : Abdurahamane Hassane
Edita : Abdullahi Tanko Bala