1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Fada ya kara kazanta a Somalia

Hauwa Abubakar AjejeDecember 22, 2006

Dakarun Gwamnatin rikon kwarya ta Somalia tare da goyon bayan dakarun Habasha suna ci gaba da fafatawa kwana na hudu a jere a kudancin Somalia,yayinda dakarun islama suka kaddamar da abinda suka kira jihadi akan Habasha.

https://p.dw.com/p/Btwu
Hoto: AP

Bangarorin biyu sun shiga kwana na hudu na fada a gabashi da kudancin birnin Baidoa,fadar gwamnatin rikon kwarya ta kasar kimanin kilomita 250 daga arewacin birnin Mogadishu.

Ministan yada labarai Ali Jama ya fadawa kanfanin dillancin labaru na AFP cewa har yanzu fada na ci gaba a wadannan yankuna,wanda a cewarsa fada yafi karfi ne a yankunan Idale da Dinsoor.

Wadanda suka ganewa idanunsu sunce tankunan yaki na kasar habasha sun rastsa cikin daren jiya zuwa garin Daynunay a gabashin kasar,sun kuma bada rahoton jin karar harbe harbe a yankin.

Dukkanin bangarorin biyu dai sunyi ikrarin yiwa juna barna na rayuka,kodayake babu takamaimen bayani na yawan wadanda aka kashe cikin wannan fada.

Gwamnatin dai tace ta kashe abokan gabanta 200 tare da raunata da daruruwa cikin kwanakin uku,yayinda dakarun islama a nasu bangare suka sanarda cewa sun kashe akalla dakarun gwamnati 70.

Ministan yada labarai jama yace,cikin dakarun islama da sojojin gwamnati suka kashe har da sojin sa kai na ketare.

Wannan fada dai yana ci gaba duk da sanarwar da komishinan agaji na KTT Louis Michel yayi cewa ya samu nasarar shawo kan bangarorin biyu na komawa tattaunawar zaman lafiya.Michel yace fada ba zai magance rikici dake tsakanin bangarorin biyu ba.

“tashe tashen hankula ba zasu magance rikici nan ba,saboda haka hanya daya kadai ake da ita wajen kawo karshenta,itace sake komawa tattaunawar zaman lafiya da aka fara a Khartoum”

Wannan fada ya janyo daruruwan jamaa suka tsere daga gidanjensu a yau jumaa yayinda daruruwan dakarun gwamnati da goyon bayan Habasha suke ci gaba da shiga da tankunan yaki domin kare fadar gwamnatin daga dakarun kotunan musulunci da suka ce sun kaddamar da jihadi kan Habasha.

Wani maaikacin agaji na MDD a garin wajid yace dubban iyalai suka tsere daga kauyukan dake kewayen Baidoa suna masu barin dabbobinsu da anfanin gona a baya,a yankunan da dakarun musluncin ke rike da su kuma rahotanni sunce daruruwan jamaa sun tsere zuwa birnin Mogadishu.

Shugaban kungiyar islama Sheikh Hassan dahir Aweys tun a jiya alhamis yayi kira ga yan kasar ta Somalia da su fito su yaki kasar Habasha wadda waadin da aka baiwa dakarunta su fice daga Somalia yak are a ranar talata.

Kasar Habasha dai tana taimakon gwamnatin rikon kwarya ce ta Somalian wadda bata da karfi domin yakar dakarun kotunan musulunci da suke rike da babban birnin kasar Mogadishu dama yankuna da daman a kasar da yaki ya daidaita.