1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Fada ya kara kazanta a Somalia

December 22, 2006
https://p.dw.com/p/BuWj

Cikin fada mafi muni ya zuwa yanzu,dakarun gwamnatin Somalia dake da goyon bayan Habasha sun kara da dakarun kotunan musulunci a kusa da hekwatar gwamnatin rikon kwaryar a Baidoa.

Dukkanin bangarorin biyu sunyi ikrarin kashe daruruwan abokan gabansu.

Shugaban kotunan islaman Sheikh Hassan dahir Aweys yai kira ga Somaliyawa da su shiga abinda ya kira jihadi akan Habasha.

Wannan fada dai wani cikas ne ga kokarin diplomasiya da jakadan Kungiyar Taraiyar Turai Loius Michel yakeyi na jayo hankalin bangarorin biyu da su koma tattaunawar zaman lafiya.

Akwai da tsoron cewa fada na iya bazuwa cikin yankin na kahon Afrika.

Wannan fada dai ya fara ne tun ranar talata bayan karewar waadin da kotunan musuluncin suka baiwa dakarun Habasha dasu fice daga kasar.