Fada ya sake barkewa tsakanin marikitan kasar Somalia
December 21, 2006Talla
Duk da shirin komawa ga shawararin samar da zaman lafiya a Somalia har yanzu ana ci-gaba da gwabza fada tsakanin sojojin sa kai na ´yan Islama da dakarun gwamnatin wucin gadi dake samun daurin gindin kasar Ethiopia. Kwana na biyu a jere, sassan biyu sun yi ta harba rokoki tare da amfani da bindigogin atileri akan juna a kusa da garin Baidoa. A jiya mai shiga tsakani na KTT Louis Michel ya ce sassan da ke rikici da juna sun nuna shirin komawa kan teburin yin sulhu don samar da zaman lafiya.