1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Fadada fagen siyasa ga matasa a Najeriya

Abdullahi Tanko Bala
February 20, 2018

Majalisar dokokin jihohi 27 na Najeriya sun amince da kudirin dokar rage shekarun takarar zabe domin bai wa matasa damar shiga a dama da su.

https://p.dw.com/p/2t0S9
Nigeria - Jugenddemonstration "not too young" in Abuja
Hoto: Uwais Abubakar Idris

A Najeriya kudurin dokar bai wa matasa damar tsayawa takara ya samu amincewar kasha 2 cikin kasha 3 na majalisun dokokin jihohin kasar, a yunkurin gyaran kundin tsarin mulki don mayar da shekarun tsayawa takarar shugabancin  Najeriyar zuwa 35 daga shekarun 40.  

Buhari Nigeria-Wahl 2015
Hoto: APC

Alummar Najeriyar dai sun fara jin kamshin gyaran tsarin mulkin kasar kasancewar ya zuwa yanzu sama da jihohi 27 suka kada kuri’ar amincewa da sauye-sauyen da ake son aiwatarwa a sassa 16 na kundin tsarin mulkin wanda ya hada da rage shekarun tsayawa takara a matakai daban daban domin bai wa matasa damar shiga a dama da su a harkokin mulki.

Matsa da suka yi ta gangami da matsin lamba don aiwatar sauyin sun shiga murnar samun nasara. Marka Amnza matashi ne a cikin masu gwagwarmayar ya bayyana muhimmancin matakin da cewa zai inganta ci gaban dimukradiyya a kasar.

Nigeria - Jugenddemonstration "not too young" in Abuja
Hoto: Uwais Abubakar Idris

A karkashin wannan tsari an rage shekarun tsayawa takara na mukamin shugaban kasa daga shekaru 40 zuwa 35, yayinda na ‘yan majalisun tarayya da jihohi aka maida shi shekaru 25, na gwamna kuma shekaru 35.

Matsan Najeriya na masu jadada cewa zasu iya samar da sauyin da ake bukata. Tuni dai shugaban majalisar datawan Najeriya Bukola Saraki ya bayyana farin ciki da samun jihohi sama da 25 da suka jefa kuri’a a kokarin gyaran kundin tsarin mulkin Najeriyar, akin da sau biyu ana wannan yunkuri ba tare da samun nasara ba.