1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Fadar Vatikan ta nuna nadama ga mummunar fahimtar da aka yiwa kalaman Paparoma

September 16, 2006
https://p.dw.com/p/BujL
Rahotanni daga fadar Vatikan sun ce paparoma Benedict na 16 ya kadu matuka cewa jawabin da yayi inda a ciki ya ambaci addinin Islama, ya ta da hankalin al´ummar musulmi. A cikin wata sanarwa da wani babban jami´in Vatikan ya karanta, Paparoman ya ce ya na girmama addinin Islama kuma ya nuna fatan cewa musulmi za su fahimci ainihin abin da ya ke nufi a jawabin na sa. Tarcisio Bertone wanda har wayau shi ne sakatare a fadar ta Vatikan ya ce shugaban na mabiya darikar Katholika ya damu matuka da yadda aka ba wa kalaman nasa wata ma´ana da ba wadda ya ke nufi ba. Al´umar musulmi a duniya baki daya sun nuna fushinsu tare da yin zanga-zangar yin tir da furucin da Benedict na 16 ya yi a wata lacca lokacin ziyarar kwanaki 6 da ya kawowa Jamus a wannan mako. Jim kadan gabanin fadar Vatikan ta ba da wannan sanarwa ta neman gafara, gwamnatin Saudiya ta nema da a yi bayani dalla dalla game da kalaman na Paparoma, wanda ya danganta adinin Islama da tarzoma.