Fafatawar gasar Olympic a Koriya ta Kudu
February 13, 2018Kasashen duniya na ci gaba da karawa tsakani a gasar Olympic na lokacin hunturu da birnin PyeongChang na Koriya ta Kudu ya dauki nauyi, tuni aka lashe lambobin yabo da dama a gasar kawo yanzu.
Kasashe: Zinare Azurfa Tagulla Jimla
Jamus 3 0 1 4
Holland 2 2 1 5
Amerika 2 1 1 4
Norway 1 4 3 8
Kanada 1 4 1 6
A wannan gasa na birnin PyeongChang wakilan da suka fito daga kasar Koriya ta Arewa na zama wadanda suka dauki hankali bisa dalilan siyasa, da zaman-tankiya da aka dade ana samu tsakanin kasar da Koriya ta Kudu da kuma Amirka. A dayan hannun kuma manyan jami'an gwamnatin Koriya ta Arewa da suka halarci gasar sun samu kekkyawar tarba.