1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Fafatawar neman lashe kofin kwallon hannu a Afirka

Mouhamadou Awal Balarabe
January 23, 2018

A kasar Gabon, tafiya ta fara nisa a kokarin kasashen Afirka na neman lashe kofin kwallon hannu na kasashen Afrika na maza karo na 23, inda aka shiga rana ta shida.

https://p.dw.com/p/2rO02
Handball Afrikameisterschaft Gabun - Algerien
Hoto: imago/Afrikimages

A rukunin A, Tunisia da Algeria sun tashi ci 25 ko ta ina a karawa da suka yi a karshen mako, lamarin da ya bai wa kasashen Larabawa damar samun matsayi na daya da na biyu da maki biyar kowacensu. Ita kuwa Gabon mai masaukin baki na a matsayi na uku da maki hudu, yayin da cKwango Brazaville ke a matsayi na hudu.

Handball Afrikameisterschaft Gabun - Algerien
Hoto: imago/Afrikimages

Ita kuwa kungiyar maza ta kwallon hannun kasar Kamaru ta yi abin fallasa inda ta kasa lashe ko daya daga cikin wasanin da ta buga, lamarin da ya sa wasan karshen da za ta yi na ran sarki ya dade ne saboda an riga an cireta a gasar. A rukuni na biyu kuwa, Masar da ke rike da kofin kwallon hannu na Afirka a yanzu ta doke Angola da 25 da 20. Lamarin da ya bata damar cike ratar maki da Angola ta yi mata tun da farko, inda a yanzu suke a matsayi na daya da maki shida kowaccensu.

Handball Afrikameisterschaft Gabun - Algerien
Hoto: imago/Afrikimages

Ita kuwa Moroko duk da cewar ta doke kunmgiyar maza na kwalon hannu na kwango, amma tana a matsayi na uku ne da maki biyu kamar takawartata. Yayin da kungiyar kwallon hannun tarayyar Najeriya ta kama hanyar ban kwana da gasar ta Afirka saboda ba ta yi nasara ko da daya a wasannin da ta yi ba.

A ranar 27 ga wannan wata na janiru ne za a yi wasan karshe na kwallon hannun a birnin Libreville, kuma kasashe uku da suka fi taka rawar gani za su wakilci nahiyar Afirka a gasar duniya ta kwallon hannu da zai a gudana a kasar Jamus a shekara ta 2019.