1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Fafutukar Jamus Ta Neman Kujera A Kwamitin Sulhu

July 19, 2004

Yau sama da shekaru goma ke nan Jamus na neman dawwamammiyar kujera a Kwamitin Sulhu na MDD da kuma neman ganin an yi garambawul ga ayyukan majalisar baki daya

https://p.dw.com/p/Bvi1

A dai halin da ake ciki yanzun kwamitin sulhu na MDD na da membobi na dindindin guda biyar, sai kuma wasu membobi goma da ba na dindindin ba. Wadannan membobi na dindindin dake da ikon hawa kujerar naki sun hada da Amurka da Rasha da Faransa da Birtaniya da kuma China. Kwamitin shi ne kawai ke da ikon wajabta kudurori akan kasashen majalisar. Ita kuma Jamus yau shekaru 31 ke nan da take karkashin tutar MDDr. Ita ce a rukuni na uku a tsakanin kasashen dake ba da gudummawa mafi tsoka ga kasafin kudin majalisar kuma a sakamakon haka tun a wajejen tsakiyar shekarun 1990 ta shiga neman dawwamammen wakilci a kwamitin sulhu. A lokacin da yake bayani game da haka tsofon ministan harkokin wajen Jamus Klaus Kinkel cewa yayi:

Har yau kwamitin sulhu na MDD na kan tsofon fasalinsa ne da ya samo tushe bayan yakin duniya na biyu ba tare da bayar da la’akari da muhimmancin da kasashen Japan da Jamus suka samu a tsakanin wannan lokaci ba. Ina mika godiya ta ga dukkan kasashen dake ba wa Jamus goyan baya domin samun dawwamammen wakilci a kwamitin sulhun na MDD.

Wannan lafazin ko da yake an gabatar da shi ne tun misalin shekaru goma da suka wuce, amma ministan harkokin wajen Jamus na yanzu Joschka Fischer na iya tu’ammali da ita. Domin kuwa har yau babu wani sauyin da aka samu a game da wannan tsofon yayi, wanda aka dade ana neman ganin an yi masa gyaran fuska. An dai shirya cewar nan da karshen wannan shekarar sakatare-janar na Majalisar Kofi Annan zai nada wani kwamitin kwararru domin bitar shawarwarin garambawul da aka bayar. To sai dai kuma abin takaici, kamar yadda ministan harkokin waje Joschka Fischer ya nunar, babu wani Bajamushe ko da kwaya daya a wannan kwamiti. Amma ga alamu shawarwarin sun tanadi karin wakilai na dindindin da wadanda ba na dindindin ba a kwamitin sulhun na MDD kuma Jamus ka iya cimma nasara bisa manufa. Domin kuwa kasar a baya ga guddummawa mai tsoka da take bayarwa, kazalika ana damawa da ita a matakan kiyaye zaman lafiya da majalisar ke dauka a sassa dabam-dabam na duniya. A matsayinta na wakiliya da ba ta dindindin ba kasar ta Jamus ta taka muhimmiyar rawa wajen hada kan sauran wakilan kwamitin ta yadda kujerar na ki ba ta da wani alfanu, inda kuma Amurka ta sha fama da radadin lamarin dangane da rikicin Iraki da kuma kai ruwa ranar da aka sha famar yi a game da kotun duniya akan miyagun lafuka. To sai dai kuma duk da nasarar da kasar ta samu har yau da walakin dangane da maganar garambawul ga ayyukan MDD ko Ya-Allah Amurka zata amince da hakan ko kuwa zata sake hayewa kujerar na ki kamar yadda lamarin ya kasance misalin shekaru goma da suka wuce.