1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Fafutukar tabbatar da adalci a Chadi

Ramatu Garba Baba
July 12, 2017

Wasu kungiyoyi a Chadi sun kirkiro da wata dabarar da ta hada kan matasa da aka yi wa lakabi da "justice or nothing” da ke faufutukar tabbatar da adalci tsantsa a fadin kasar.

https://p.dw.com/p/2gNzr
Tschad Präsident Idriss Deby
Hoto: Getty Images/F.Belaid

Irin kalubalen da ake fuskanta na aikata rashin adalci a kasar ta Chadi shi ne makasudin kirkiro wannan kungiya a kasar ta Chadi. Matasan da suka kirkiri wannan kungiya suka ce ''mu ba wai dalibai ba ne kawai mun 'yan Chadi ne da ya kamata al'umma su zo mu hade wuri guda don yakar rashin adalci''.

Kungiyar ta tsara hanyar jan hankalin hukumomi ta hanyar bore ko shiga yajin kin cin abinci da kuma shigar da kara gaban kuliya. Sai dai kungiyar za ta fi mayar da hankali ne a kan kare yancin dalibai kamar yadda kakakin kungiyar Noel Ndildoume ya bayyana inda ya ce ''kungiyar adalci na tare da ku a wannan lokacin, a baya mun sha shiga tsakaninku da gwamnati don ganin an warware matsalarku''.

Watanni da dama dalibai suka kwashe suna zanga-zanga don nuna bacin ransu kan yadda aka dakatar da karatu a Jami'ar inda aka sami barkewa rikici, Noel Ndildoume da sauran masu rajin kare yancin  dan adam sun sanya hannu kan kudirin da zai mutunta damar gudanar da zanga-zangar lumana, ya kuma ce sun yi hakan koda gwamnati ta ki amincewa da  bukatar ba za su yi kasa a gwiwa ba.