1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Falasdinu ta maida martani ga harin Juma'a

Ramatu Garba Baba
July 14, 2017

Shugaban Falisdinawa Mahmoud Abbas ya soki harin da aka kai a kusa da masallacin Kudus da ya halaka 'yan sandan Ira'ila.

https://p.dw.com/p/2gZmc
Israel Tempelberg in Jerusalem
Hoto: Getty Images/AFP/T. Coex

Shugaban Palisdinawa Mahmoud Abbas ya yi Alla-wadai da harin da aka kai a wannan Juma'ar  kusa da masallacin Kudus da ya halaka wasu jami'an 'yan sandan Isra'ila biyu. A daya bangaren Firaiministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya ce za su dauki duk mataki don tabbatar da tsaro a yankunansu, Netanyahu ya fadi hakan ne a a tattaunawar da suka yi da Abbas ta wayar tarho.

Al'amarin ya sanya dakatar da Sallar Juma'a a masallacin birnin Qudus a sakamakon harin da ya yi sanadiyar rayukan 'yan sandan Isra'ila biyu da kuma mahari guda. Masallacin dai shi ne wajen ibada na uku mafi girma da musulmi ke gudanar da Sallar Juma'a a kowace Juma'a.

An dai dauki matakin rufe masallacin ne saboda dalilai na tsaro, harin ya kuma kasance hari mafi muni da aka kai a birnin na Jerusalem a baya-bayan nan. Wajen da aka kai harin na yau na da matukar mahinmanci ga dukannin Yahudawa da musulmi, ya kuma kasance wani wurin zaman dar-dar sanadiyar takadamar da ke a tsakanin Isra'ila da Palisdinu.