1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sabon rikici tsakanin Falatsinawa da 'yan sandan Isra'ila

Yusuf BalaSeptember 28, 2015

An dai jibge jami'an 'yan sanda a harabar masallacin Al-Aqsa inda Yahudawan ke zuwa ziyara a matsayin wuri mai tsarki ga masu ibadarsu.

https://p.dw.com/p/1GeTB
Jerusalem Al Aqsa Moschee Auseinandersetzung Polizei
Hoto: Ahmad Gharabli/AFP/Getty Images

A ranar Litinin din nan fada ya sake barkewa tsakanin 'yan sandan Isra'ila da Falatsinawa a harabar masallacin Al-Aqsa, kamar yadda mai aika wa kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP rahoto ya bayyana, wani abu kuma da ke kara haske kan yiwuwar kara kazantar rikici a daidai lokacin da ake shirin shiga hutun bukukuwan Sukkot da Yahudawa ke yi.

An dai jibge jami'an 'yan sanda a harabar masallacin inda Yahudawan ke zuwa ziyara a matsayin wuri mai tsarki ga masu ibadarsu, haka nan kuma wuri mai tsarki ga mabiya addinin na Islama.

A ranar Lahadi ma dai an dan gwabza da jami'an tsaron da ke kan iyaka bayan da matasan Falatsinawan suka rika jefa duwatsu ga 'yan sanda inda su kuma suka mai da martani ta hanyar amafani da hayaki mai sa hawaye suka tarwatsa su.