1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Fallasa yaƙin Afganistan

August 13, 2010

Za'a wallafa ƙarishen bayanen sirri kan yaƙin Afganistan ,duk da hanin da gwamnatin Amirka ta yi wa kafar sadarwa ta Wikileak.

https://p.dw.com/p/OmjL
Wani Makamin da NATO ta harba a AfganistanHoto: AP

Mutumin da ya kafa kafar sadarwa ta Wikileaks dake ƙasar Amirka, yace zai wallafa sauran takandun ƙarshe da suka samo daga dakarun sojin Amirka, waɗanda ke fallasa ayyukan sojojin a yaƙin da suke yi a Afganistan, duk kuwa da rokon da Washington ta yi, na lallai sai su boye bayanen. Julian Assange a wani taron manema labarai, ya bayyana cewa shafin nasu ya shirya tsab don wallafa sauran kopi dubu 15, na takardun sirri da ya samo, waɗanda kuma bai kai ga ƙarisa wallafasu ba. A halinda ake ciki ma'aikatar tsaron Pentagon tace, wannan zai kasanca babban kusukure, ace kafar yaɗa labaran ta wallafa bayanen sirri dake hannun ta. Ƙungiyar kare 'yan jaredu, ta Reporters Without Borders wanda ta yaba da irin gudumawar da shafin Wikileak ke bayarwa, ta suke lamarin fitar da bayanen, inda tace hakan zai sa rayukan fararen hula dake tallafawa a yaƙin Afganistan cikin haɗari.

Mawallafi: Usman Shehu Usman

Edita: Umaru Aliyu