1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Fallasar lekan asiri na Amurka game da Iraqi

April 7, 2006
https://p.dw.com/p/Bv2j

Wani tsohon mai bada shawar ga mataimakin shugaban kasar Amurka Dick Chaney,yace,shugaba Bush ne ya bada umurnin a saki wasu muhimman bayanai game da Iraqi ga kafofin yada labarai na kasar.

Bisa wasu bayanai na kotu,cikin karar da aka shigar,jamiin na fadar Amurka,lewis Libby,ya kuma bada shaidar cewa,mataimakin shugaban amurkan ya ba shi umurnin yayi magana da kafofin yada labarai game da wasu bayanan leken asiri game da Iraqi da kuma tsohon jakadan Amurka Joseph Wilson wanda ya soki lamirin manufofin Bush akan Oraqi.

Ana zargin Libby da laifin cin amanar kasa da kawo cikas ga harkokin sharia,bayab wani bincike da akayi game da bayanai da suka tabbatar da cewa uwargidansa jamiar leken asiri ta Amurka ce.

Tun farko,Bush ya tada jijiyoyin wuya cewa an fallasa wannan asiri ba tare da sanin sa.