1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Fara mayar da bakin haure Turkiya

Abdourahamane Hassane/SBApril 4, 2016

Kasar Girka ta fara jigilar 'yan gudun hijira wadanda ba su cikin ka'ida zuwa Turkiya karkashin yarjejeniyar da aka kulla tsakanin kasashen Turai da Turkiya.

https://p.dw.com/p/1IPC0
Türkei Dikili Rückführung von Flüchtlingen
Hoto: Getty Images/AFP/O. Kose

Kamar yadda yarjejeniyar da aka cimma tsakanin Turkiyya da Kungiyar tarrayar Turai ta tanada a kan tallafa wa Turkiyya da kudade domin ta sake karba yan gudun hjira.Kawo yanzu dai jiragen ruwa guda uku suka tashi daga tsibirin Lesbo na Girka dauke da 'yan gudun hijira galibi na kasashe Pakistan da Bangladesh domin isa a tsibirin Dikili na Turkiya.

Türkei Dikili Rückführung von Flüchtlingen
Hoto: Getty Images/AFP/O. Kose

Kuma yanzu haka jirgin ruwa na farko ya sauka a tsibirin Dikile da wasu 'yan gudun hijirar gami da bakin haure wadanda jami'an tsaro ke yi wa rakiya.

Sama da 'yan gudun hijira dubu uku ke tsibirin Lesbo na Girka wadanda kuma dama daga ciki za a kwashe zuwa tsibirin Dikili na Turkiya tsibirin da bisa ga dukkan alamu ba shi da isasssun wurare na karbar bakin kamar yadda magajin garin tsibirin Mustafa Turun ya nunar.

Dubban jama'a da 'yan kungiyoyi masu fafutuka suka gudanar da zanga-zanga a kan ruwan da ake kwashe 'yan gudun hijira suna raira irin wadannan kallamu na ganin cewar an dakatar da mayar da bakin haure da 'yan gudun hjira zuwa Turkiya.

Griechenland Die Situation der Flüchtlinge auf Lesbos
Hoto: DW/R. Shirmohammadi

Kungiyar kare hakin bil Adama ta Amnesty International tare da wasu sauran kungiyoyin kare hakkin jama'a wadanda tun farko suka yi Allah wadai da yarjejeniyar tsakanin Turkiya da kungiyar ta Tarayyar Turai ta bayyana damuwa kan wannan al'amari.