1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Faransa na kwashe bakin haure a Calais

October 24, 2016

Kasar Faransa ta jibge jami'an tsaro a sansanin 'yan gudun hijirar Calais don gudanar da aikin rufeshi baki daya, Sai dai mazauna sansanin sun yi Allah wadarai da matakin bisa zargin rashin tanadar da sabbin matsugunai.

https://p.dw.com/p/2RcSK
Frankreich Räumung Dschungel von Calais
Hoto: picture-alliance/AP Photo/E. Morenatti

'Yan gudun hijirar sun kasance cikin rudani bayan da suka tabbatar da za a rabasu da mazaunin da suka shafe tsawon lokaci a ciki. An dai tanadi manyan bas-bas akalla 60 da za su yi jigilar 'yan gudun hijirar maza da mata hada yara kanana daga wannan sansani i zuwa cikin birni don duba lafiyarsu sannan a kaisu wasu wuraren wucin gadi da zasu zauna. Sai dai mazauna wannan sansani na Calais zasu tashi ne ba a son ransu ba, kamar yadda wani dan Sudan ke cewa: " Wannan  kasar matsala ce, ga shi yanzu zasu kwashemu i zuwa babban birni ba tare da sanin asalin inda za mu kwana ko abin da zamu ci ba."

Mafi yawan mazauna wannan sansani na Calais 'yan asalin Afghanistan ne da Iritiriya da kuma Sudan da suka mai da sansanin tashar masu akidar zuwa wasu kasashen Turai ta hanyar likewa a jikin manyan motoci da ke dakon kaya. Wani da ya tattara nasa ya nasa ya ce babban kalubale da suke fukanta shi ne rashin samun dama daga jami'an tsaro da ke kan iyakar Faransa tsallakawa zuwa Birtaniya. Ya ce "Ina samun matsalar shiga Birtaniya sabo da 'yan sandan Faransa na tsananta bincike, Kuma an dau hotunan tambarin yatsarmu a Italiya wanda kuma ke zama barazana in muka je Birtaniya dan gwamnatin Birtaniya zata maidomu Italiya inda asalin tambarin yatsunmu ya nuna. "

Frankreich Räumung Dschungel von Calais
Ana fara rejistar bakin haure na Calais kafin a kwashesuHoto: Reuters/P. Woyazer

Wasu da dama na takaicin rabuwa da sansanin ganin yadda ya zama silar zumunci tsakanin 'yan gudun hijira. Amma ya zama wajibi a rufe sansanin a cewar Fabienne Bucco daya daga cikin jami'an da ke aikin bayyana yadda aikin ke gudana. Ta ce "Kawo yanzu aikin na tafiya a tsanake, babu wata matsala, kuma 'yan gudun hijira na bamu hadin kai babu hatsaniya. Amma dai mun fi mai da hankali ga marasa rinjaye kamar yara kanana da mata. A yau dai muna sa ran tafiya da mutane 2,500"

Tun shekarun 1990 ne 'yan kasashe da dama ke yada zango a arewacin Calais inda ya zama sansanin 'yan gudun hijira da ya yi kaurin suna ga bakin haure da ke son zuwa Birtaniya. Sai dai hukumomin agaji sun koka kan yadda rayuka sama da 8000 ke cunkushe wuri guda.