1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Faransa ta ce a shirye ta ke ta tura dakaru dubu 2 zuwa kudancin Libanon

August 25, 2006
https://p.dw.com/p/Bulf

Ministocin harkokin waje na kasashen KTT zasu gana yau juma´a a birnin Brussels don tattaunawa akan karo karon da kungiyar mai membobi 25 zata bayar ga sabuwar rundunar kiyaye zaman lafiya ta MDD da za´a girke a kudancin Libanon. Babban sakataren MDD Kofi Annan zai halarci gun taron na ministocin harkokin wajen. Taron dai ya zo ne kwana guda bayan da shugaban Faransa Jacques Chirac ya ba da sanarwar cewa a shirye kasarsa ta ke ta ba da gudunmawar sojoji dubu 2 ga rundunar ta MDD. Faransa dai ta sha suka na tayin ba da sojoji 200 da farko. Shugaba Chirac ya ce Faransa wadda ke jagorantar tawagar MDD a kudancin Libanon, a shirye ta ke ta shugabanci sabuwar rundunar. Faransa ta kara yawan sojojin ne bayan da Italiya ta yi alkawarin tura sojoji kimanin dubu 3 sannan kuma ta yi tayin jagorantar dakarun na MDD.

Shugaba Chirac ya ce:

“Faransa ta samu tabbaci daga Isra´ila da Libanon da kuma MDD cewa game da aiki da kuma kariya ga rundunar UNIFIL da za´a fadada ta a kudancin Libanon.”