1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Faransa ta karrama gawar Arnaud Beltrame

Gazali Abdou Tasawa
March 28, 2018

Faransawa sun gudanar da taron karrama Arnaud Beltrame jami'in tsaron da ya sadaukar da ransa wajen ceto wata mata da wani dan ta'adda ya yi garkuwa da ita.

https://p.dw.com/p/2v8fN
Frankreich Gedenkfeier für den getöteten Polizisten Arnaud Beltrame
Hoto: Reuters/C. Hartmann

A kasar Faransa an gudanar a wannan laraba da taron karrama gawar Kanal Arnaud Beltrame jami'in tsaron da ya sadaukar da ransa wajen ceto wata mata da wani dan ta'adda ya yi garkuwa da ita a lokacin wani harin ta'addanci da ya kai a ranar Juma'ar da ta gabata a garuruwan Carcassonne da Trebes inda mutane hudu suka hallaka. 

Daruruwan Faransawa ne dai da suka hada da iyali, dangi, 'yan uwa da aminnan arziki na marigayin suka hallara a wajen taron karramagawar mamacin da ya gudana a birnin Paris a safiyar wannan Laraba. Da yake jawabi a wajen wannan taro, Shugaba Emmanuel Macron na Faransa ya bayyana Kanal Aranaud Bertrame a matsayin jarumi. 

A gobe Alhamis ne dai za a gudanar da jana'izar marigayin a garin Ferrals a kudancin Faransa. A ranar Juma'ar da ta gabata ce dai wani matashi mai suna Radouane Lakdim ya hallaka jami'in tsaro wanda ya amince ya mika kansa gareshi a madadin wata mata da ya yi garkuwa da ita.