1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Faransa ta kwaso dattin masana'antu mai guba daga Côte d'Ivoire.

YAHAYA AHMEDNovember 7, 2006

Faransa ta fara kwaso dattin masana'antu mai gubar da aka jibge a ƙasar Côte d'Ivoire, wanda ya janyo asarar rayukan mutane 10 a birnin Abidjan a cikin watan Agustan da ya gabata.

https://p.dw.com/p/BvTA
Aikin kwashe dattin masana'antu mai guba a Côte d'Ivoire
Aikin kwashe dattin masana'antu mai guba a Côte d'IvoireHoto: AP

Jirgin ruwan, mai suna „MN Toucan“, ya iso tashar jirgin ruwan Le Havre jiya da safe ne ɗauke da Container ɗari da 41, waɗanda a cikinsu ne aka kwaso dattin masana’antu mai gubar daga ƙasar Côte d’Ivoire. A gaban ministan kare muhalli ta Faransa, Nelly Olin ne aka fara sauke su. Ko me za ta iya faɗa game da wannan matakin da gwamnatin Faransan ta ɗauka? , duk da cewa wani kamfanin ƙasar Holland ne ke da laifin jibge dattin a can Côte d’Ivoire din?:-

„Isowar jirgin a nan dai na alamta zumuncin da muke nuna wa Côte d’Ivoire ne. Al’ummanta sun galabaita. An sami kuma mutane da dama, waɗanda illar ta shafa. Abin ban takaici ne dai.“

Dattin dai ba daga Faransa yake da asali ba. Wani kamfanin ƙasar Holland ne ke da laifin jibge shi a can Côte d’Ivoire ɗin. Sai Faransan ta bayyana shirinta ne na kwaso shi daga can, bayan mutane sun rasa rayukansu, sa’annan da dama kuma suka yi ta fama da cututtuka daban-daban. A cikin makwannin da ke zuwa nan gaba ne kuma, za a kwaso sauran Container guda 4 na dattin.

A cikin watan Agustan da ya gabata ne dai kamfanin ƙasa da ƙasar nan Transfigura, da ke cibiyarsa a ƙasar Holland, ya jibge dattin masana’antu mai guba kimanin tan ɗari 5 a birnin Abidjan, ba tare da ɗaukan matakan kare lafiyar jama’a ba. Illar da da gubar ta janyo dai, ta yi sanadiyar mutuwar mutane 10, yayin da dubbani kuma suka kamu da cututtuka masu nasaba da wannan gubar, a cikinsu kuwa har da yara ƙanana. A halin yanzu dai, an ɗaukaka ƙarar kamfanin a Kotu, don neman ya biya diyya ga waɗanda suka galabaita. Game da wannan matsalar dai, wani ƙwararren masani kan dattin masana’antu mai guba, kuma jami’in ƙungiyar nan ta Greenpeace a Faransan, Yannick Vicaire, ya bayyana cewa:-

„A halin yanzu dai muna tsakiyar wata matsala ne, wat ta yadda za mu yi ta kau da dattinmu. Ya kamata kuwa wannan lamarin ya sanya mu cikin wani tunani mai zurfi, ba kan taɓargazar jibge dattinmu mai guba a ƙasashen Afirka kawai ba, amma kuma kan tambayar, wai shin me ya sa ba ma iya rage yawan dattin da muke samarwa ne?“

Daga tashar jirgin ruwan Le Havre dai, za a dinga jigilar Contanonin dattin ne a hankali, a kan jiragen ƙasa zuwa wani gun da za a ƙona shi a kudancin birnin Lyon. To a nan ma, ƙungiyar Greenpeace ta ce da akwai kasada. Kamar dai yadda Yannick Vicaire ya bayyanar:-

„Abin da dai za a iya cewa a nan shi ne, Faransa, musamman mazauna jihar Izère, za su yi ta fama ne da shaƙar ƙurar da za ta taso daga dattin da aka ƙonan. Ƙona dattin dai ba wata gwaninta ba ce. Ba zai sa gubar ta ɓace hakan nan ba. Za ta zama ƙura ne ta bi iska, wadda kuma mutane za su yi ta shaƙa.“

A can Côte d’Ivoire ɗin dai, wasu manajojin kamfanin na Transfigura guda biyu, dukkansu Faransawa, na tsare a hannun jami’an tsaro. Ana zarginsu ne da safarar dattin masana’antu mai guba zuwa ƙasar a haramce. Jami’in ƙungiyar Greenpeace Vicaire dai na son ganin cewa, an koyi darasi daga wannan taɓargazar, ta yadda kuma, za a dinga inganta hanyoyin sa ido kan zirga-zirgan jiragen ruwa, da kuma kayan da suke ɗauke da su:-

„Ina fatar ganin cewa, za a gano duk waɗanda ke da hannu a cikin wannan maguɗin, a kuma hukuntad da su. A siyasance kuma, an koyi darasi na farko, amma hakan bai wadatar ba. Kamata ya yi a biya jama’ar birnin Abidjan da wannan lamarin ya shafa diyya. To bayan haka ne za a iya cewa, an nuna adalci.“