1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Faransa ta tabbatar da nauín kwayar cutar H5N1 a cikin kasar ta

February 25, 2006
https://p.dw.com/p/Bv6i

Faransa ta tabbatar da cewa an sami nauín kwayar cutar H5N1 ta masassarar tsuntsaye a wata gonar kiwon kaji dake gabashin kasar. Wannan dai shi ne karon farko da aka sami bullar cutar a wata gonar kiwon kaji a nahiyar turai da kuma zai kassara harkar kiwon kajin a kasar Faransa. A waje guda kuma Ministocin lafiya na kasashen kungiyar tarayyar turai sun sanar da cewa zasu kaddamar da wani gagarumin shirin fadakarwa da wayar da kai a daukacin nahiyar turai a game da yaduwar cutar murar tsuntsaye. Ministocin sun baiyana cewa makasudin gangamin shi ne domin fadakar da jamaá a game da fargabar da ake baiyanawa dangane da cutar da kuma kwantar da hankulan jamaá a game da batun yiwuwar yaduwar cutar a tsakanin jinsin bil Adama. An sami bullar nauín cutar murar tsuntsayen ta H5N1a kasashe da dama na nahiyar turai. A nan Jamus a karon farko an sami bullar nauín kwayar cutar ta H5N1 a kudancin kasar.