1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Faransa za ta haramta wa mata yin lulluɓi.

April 30, 2010

Ƙasar Faransa na shirin kafa tsattsaurar doka da za ta haramta wa mata sanya niƙabi a baynin jama'a.

https://p.dw.com/p/NB4G
Matan da ke sanya niƙabi a Fransa.Hoto: Dzevad Sabljakovic

ƙasar Faransa na shirnin bin sahun takawarta ta Beljium wajen haramta wa mata sanya lulluɓi mai rufe fiska da aka fi sani da suna niƙab. Gwamnatin Nicholas Sarkozy ta yi alƙawarin miƙa ma majalisar dokokin ƙasar ƙudirin doka ,da ya tanadi hukunta duk waɗanda za a samu da amfani ko kuma sa a yi amfani da lullubin mai rufe fiska a cikin jama'a.

Idan majalisar ta albarkanci ƙudirin cikin watanni biyu masu zuwa, taran Euro dubu 15 mai gidan da zai tilasa wa mai ɗakinsa sanya niƙabi zai biya, yayin da za a ci matar da ta yi amfani da wannan nau'in na lulluɓi a baynan jama'a tarar Euro 150.

Ita dai Beljium da ta zama da ƙasar Turai ta farko da ta haramta sanya niƙabi, ta tanadi hukunci kwanaki bakwai a gidan yari, da kuma tarar Euro 25 ga duk waɗanda za su keta dokar da ta shafi niƙabi.

Mawallafi: Mouhamadou Awal

Edita: Umaru Aliyu