1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Fararen hula dake mutuwa a Afganistan

August 10, 2010

Yawan Fararen hula dake mutuwa a yaƙin ƙasar Afganistan, ya ƙaru fiye da kima

https://p.dw.com/p/OhVz
'Yan Afganistan gaban gawakin 'yan uwansu da aka kashe.Hoto: AP

Wani rohoton da MDD tafitar kan yaƙin Afganistan, yace kashe fararen hula ya ƙaru da kashi 30 cikin ɗari a wotanni shida na bana. Inda rohoton yace masu tada ƙayar baya, sun fi hallaka fararen hula, idan aka kwatanta da sojojin ƙungiyar tsaro ta NATO. Itama a rohoton tsakiyar shekara da ta bayar, rundunar tsaron ta dakarun ƙawance, tace tana lissafin an hallaka fararen hula fiye da dubu ɗaya a wattani shida na bana kaɗai. A jiya ne dai wata ƙungiyar agaji ta fitar da sunayen ma'aikatanta takwas, da akayiwa kisan ƙilla a arewacin ƙasar ta Afganistan, bayan da Taliban tace itace ta hallaka mutanen, domin zargin suna yaɗa kiristanci ne.

Mawallafi: Usman Shehu Usman

Edita: Zainab Muhammed Abubakar