1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Farautar yan tawayen Maimai a Jamhuriyar Demokradiyar Kongo

November 24, 2005
https://p.dw.com/p/BvJg

Dakarun gwamnati a Jamhuriya Demokradiyar Kongo, sun shiga ba ji ba gani,farautar yan tawayen maimai, da ke hadassa ta´assa a yankin Katanga, na kudu maso gabacin kasar.

Rahotani sun nunar da cewa daga farkon watan da mu ke ciki zuwa yanzu, sojoji masu biyyaya ga gwamnati sun kashe daruruwan yan tawaye.

Tun shekara ta 2003 a ka kawo karshen yaki a wannan kasa to saidai har yanzu tsugune ba ta kare ba, dalili da wasu gungun yan tawaye da ke ci gaba da gana azaba ga jama´ar yankin, duk da kasancewar dakarun shiga tsakani na Majalisar DinkinDunia su kimanin dubu 17 da ke jibge.

Kakakin gwamnatin Jamhuriya Demokradiyar Kongo, ya sannar da a wannan karo babu gudu babu ja da baya ,sai rundunar soja ta kasa, tare da hadin gwiwar sojojin Majalisar Dinkin Dunia sun ga bayan yan tawayen maimai.