1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rashin tabbas a garin Damasak da kewaye

Al'Amin Suleiman Mohammad / MNAJuly 15, 2015

Jama'a na tserewa daga garin Damasak da kuma wasu kauyka da ke kusa bayan da suka bayyana cewa sojojin Chadi da Nijar da ke kula da wuraren sun fara ficewa daga yankin.

https://p.dw.com/p/1Fyy5
Boko Haram Flüchtlinge
Hoto: DW/K. Gänsler

A farkon watan Maris na wannan shekara ne dai sojojin Chadi da Nijar suka ayyana cewa sun kwato garin Damasak daga mayakan Boko Haram da suka karbe iko da shi inda kuma suka zauna zuwa wannna lokaci.

Mazauna yankin sun bayyana cewa sojojin sun shaida musu cewa babu wani sojan Najeriya da ya je wannan yanki abin da ya sa suka bada dalili na kwashe na-su ya na-su daga wajen don komawa kasashensu.

Wannan ya sa mutanen garin Damasak da kauyuka da ke kewaye ficewa daga yankin saboda gudun abin ka iya samun su in sun ci gaba da zama ba tare da jami'an tsaro a yankin ba.

Kaura daga Damasak saboda fargaba

Yawancin wadanda suka tsere daga yankin Damasak din sun nufi yankunan da ke cikin Jamhuriyar Nijar da kuma sassan Najeriya sun kuma bayyana cewa ba za su iya zama a wuraren da babu jami'an tsaro ba.

Kampf gegen Boko Haram Nigeria
Sojojin da aka girke don yakar Boko HaramHoto: picture-alliance/dpa/Ngala Chimtom

Malam Muhammad Modu Wan-Wan wani dan Damasak ne da yanzu haka ya isa garin Maiduguri bayan tserewar da yayi ya yi wa wakilinmu na Gome Al'Amin Suleiman Mohammed karin bayani ta wayar tarho cewa sojojin Nijar da Chadi ne suka ba su shawara da su tashi daga garin.

Bayanai da yanzu haka ke fitowa daga garin na Damasak na nuna cewa bayan ficewar jama'a da jami'an tsaron, mayakan Boko Haram sun afka wa garin inda suka kona wasu sassan na garin.

Wani mazaunin yankin da bai so a bayyana sunansa ba ya ce dole ne jama'a su gudu daga garuruwan matukar jami'an tsaron ba sa nan.

Yawan 'yan gudun hijira ya karu a yankin

Tserewar da jama'a ke yi dai ya kara yawan 'yan gudun hijira musamman a jihohin Borno da Yobe inda ake fargabar kara cabewar harkokin rayuwar 'yan gudun hijrar.

Lebensmittelspenden Nigeria
Kayan abinci ga 'yan gudun hijiraHoto: DW/K. Gänsler

Dan gane da halin da 'yan Damasak da sauran 'yan gudun hijira ke cike kuma Malam Modu Wan-Wan ya ce suna cikin mawuyacin hali.

Wannan yanayi dai na zuwa ne jim kadan bayan da Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya nada sabbin hafsoshin tsaro da ake ganin sun gaji aiki mai matukar wuya.

Ya zuwa yanzu dai jami'an tsaron na Najeriya ba su fito sun karyata ko kuma gaskata wadannan rahotanni da ke nuna cewa sojojin Chadi da na Nijar sun kwashe ya nasu daga Damasak ba.