1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Fargaba game da zaɓen Gini

November 6, 2010

Al'ummar Gini na cikin rashin tabbas game da makomar ƙasar bayan zaɓen shugaban ƙasa na wannan Lahadi

https://p.dw.com/p/Q0eJ
Wata mata na jefa kati a zagaye na farko na zaben shugaban GiniHoto: picture alliance/dpa

Ana ci gaba da zaman ɗar ɗar a ƙasar Gini a dai dai lokacin da ƙasar ke jajiberin jefa ƙuri'un zaɓen shugaban ƙasa ta hanyar dimoƙraɗiyya, bayan tsawon kusan rabin ƙarni a ƙarƙashin mulkin kama karya, sai dai kuma babu jawabai irin na gangamin yaƙin neman zaɓen da aka tsara. Al'ummar ƙasar ta Gini na fargabar irin yadda zaɓukan na wannan Lahadin za su kasance sakamakon tashe-tashen hankulan dake da nasaba da na ƙabilancin da suka biyo bayan zagaye na farko na zaɓen shugaban ƙasar.

Tuni dai 'yan takara biyun da za su fafata a zagaye na biyu na zaɓen, wato Cellou Dalein Diallo da Alpha Konde suka yi kira ga magoya bayan su da su rungumi ɗabi'ar zaman lafiya da lumana a yayin da ƙasar take ƙoƙarin komawa ga tafarkin dimoƙraɗiyya. A safiyar wannan Lahadin ne dai al'ummar Gini ke zuwa runfunan zaɓen, bayan ɗage lokacin yin sa har sau biyu a can baya.

Mawallafi : Saleh Umar Saleh

Edita : Muhammad Nasir Awal