1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

141010 Israel Ahmadinedschad

October 14, 2010

Al'ummar Isra'ila dake zama a kusa da ƙauyen da Shugaban ƙasar Iran ke ziyarta suna bayyana ra'ayoyinsu, da tasirin Iran a ƙasar Lebanon.

https://p.dw.com/p/Pe9m
Ahmadinejad ya karɓi kyautar Dakta a LebanonHoto: AP

A ci gaba da ziyarar tarihi da yake yi a ƙasar Lebanon shugaban ƙasar Iran Mahoud Ahmadinejad a yaune ya ke ziyarar wani ƙauye dake kan iyakar Isra'ila da Lebanon. Wannan ƙauyen dai an ragargaza shi lokacin yaƙin Isra'ila da Hizbollah a hekaru huɗu da suka gabata. Kuma ƙasar ta Iran ta bada kuɗi aka sake gina ƙauyen. To shin ko ya ya matsauna kan iyakar daga ɓangaren Isra'ila ke kallon wannan ziyara.

Kusan dai ɗaukacin 'yan Isra'ila na ta yin magana kan wannan ziyarar, to amma mazauna kusa da yankin da Ahmadinejad zai kai ziyara waɗanda ke ƙauyen Metulla su sukafi bayyana ra'ayoyin su. Efart daliba ce dake bada abinci a hotel, tace lallai yanzu sun ƙara firgita da ziyar ta shugaban ƙasar Iran, ganin cewa yanzu gashi har a bakin ƙorar Isra'ila.

Iran Mahmud Ahmadinedschad Libanon Beirut Plakat Flash-Galerie
Hotunan Ahmadinejad a BeirutHoto: AP

"Wannan shi ne abinda mutane ki tunani, kar ka ƙara kar ka daɗa, akwai masu hushi akwai kuma waɗanda ke a tsorace. A wani abu da ba za a zata zai faru ba. Iyakar maganar kenan"

Tun da farko dai kafafen yaɗa labaran Isra'ila, sun yi ta yayata batun ziyar da Ahmadinajad zai kai maƙobciyar ta su, inda suke bayyana nasarar da shugaban na Iran zai samu. Gilad wani matashi ne dake aikin malanta.

"Ina tunanin cewa babban manufar ziyarar shine tsokala, bawai ziyarace ta Allah da annabi ba harma da takala, kuma wannan aikin banzane"

Wannan ziyara da Ahmadinejad ya kai har iyakar ƙasar Isra'ila dai, wata alama ce ya ke son ya bayyana wa Isra'ila cewa, barazanar soji da suke yi wa ƙasar sa, ba wani abu bane a gare shi. Kamar yadda wannan mai saida barasa ya ke cewa.

"A ganina musabbabin zuwa har kusa da mu shine, faɗawa duniya cewa dakarun sojin Hizbollah basa ƙarƙashin ikon gwamnatin Lebanon, amma suna ƙarƙashin Iran. Na tabbata wannan shine kawai dalilin da zai kawo shi wannan ƙauye dake kusa da mu, bawai ya zo ƙauyen don gasaitarsa ba"

Ahmadinedschad im Libanon
Tauwagar Ahmadinejad da isa BeirutHoto: AP

Da yammacin yaune dai ake saran shugaban ƙasar ta Iran zai gana da jagoran Hizbollah Hassan Nasarullah, inda ake saran Nasarullah zai tsaya kafaɗa da kafaɗa tare da Ahmadinejad, inda za su zagaya birnin Beirut tare. A jiya ma dai Ahmadinejad ya samu gagarumar tarba, inda ya ratsa cikin birnin Beitur a wata buɗaɗɗiyar mota, yana gaida dubban mutanen da ke ɗauke da tutar ƙasar Iran.

Mawallafa: Usman Shehu Usman da Clemens Verenkotte

Edita: Ahmadu Tijjani Lawal