1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Fargabar barkewar sabon yaki a Gabas ta Tsakiya

Mahmud Yaya Azare GAT
April 12, 2018

A dai-dai lokacin da Amirka da kawayenta ke aika jiragensu na ruwa masu dakwan jiragen yakin sama zuwa yankin Gabas ta Tsakiya, ana sake shiga cikin halin zaman dar-dar kan fargabar barkewar sabon yaki a Siriyan.

https://p.dw.com/p/2vxFb
USA Kitty Hawk Class aircraft carrier-Flugzeugträger
Jiragen ruwa da ke dakon jiragen yaki na Amirka na kan hanyarsu ta zuwa SiriyaHoto: picture-alliance/newscom/MC3 K.D. Gahlau

 A yanzu dai a iya cewa ta faru ta kare, an yi wa mai dami daya sata, lokaci kadai ake jira na fara abin da Amirka da kawayenta suka kira matakan daukar fansa kan Siriya, bayan da suka gama hakikance cewa, ita ce ke da alhakin kai hari da makamai masu guba a garin Douma. A yayin da Firaministan Birtaniya Thereza May ta fara zaman gaggawa da majalisarta don fayyace zabin da kasar za ta dauka, shi ma shugaba Emanuel Macron na Faransa ya bayyana cewa kasarsa ta samu isassun dalilai da ke tabbatar da cewa, dakarun Shugaba Asad ne suka kai harin da makamai masu gubar. Shi kuwa madugu uban tafiyar, Shugaba Donald Trump na Amirka cewa yake nasa binciken ya nuna har da hannun Rasha aka kai wannna harin, in ji kakakin fadar mulkinsa, Sarah Sanders. A hanu guda kuma kasar Iran ta lashi takobin fatattakar Amirka daga yankin baki daya. Su kuwa 'yan kasar ta Siriya, ci gaba suke da nuna goyan bayansu ga gwamnatinsu.

Wanne mataki za a dauka kan Siriya?

Syrien Ost-Ghouta
Shugaba Bashar al-Assad na Siriya yayin ziyarar sojojinsa a gabashin GhoutaHoto: picture-alliance/dpa/SalamPix

Masharhanta dai na hasashen cewa zabukan ka iya zama takunkumi, ko kuma kafa kwamatin bincike na musamman don tabbatar da cewa, an gama raba Siriya da makamai masu guba, lamarin da Rasha ke adawa da shi, wacce ta ce bincikenta ya tabbatar da cewa, ba a yi amfani da makami mai guba a Douma ba. Kuma wasu daga cikin kungiyoyin agaji ne ke shirya abun da ta kira wasan kwaikwayo mai abun takaici, don cimma maradunsu na siyasa. Zabi na karshe shi ne kai hare-haren ragargaza karfin sojin saman Siriyan, wanda ga dukkan alamu shi ya fi tsima Shugaba Trump bayan da ya fada wa Rasha da ke barazanar kare Siriya cewa ta saurari ruwan hatsabiban rokokin da ba ta taba ganin irinsu ba. Lamarin da ya sanya kasar Boliviya yin kira ga kwamatin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya da ya gudanar da zaman gaggawa don yin rigakafin kasadar barkewar yakin duniya ba gaira ba dalili.