1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Fargabar bazuwar rikicin siyasar Burundi

Ahmed SalisuAugust 7, 2015

Majalisar Dinkin Duniya ta ce akwai yiwuwar rikicin siyasar Burundi ya bazu zuwa wasu sassan yankin tsakiyar Afirka muddin ba a tashi tsaye wajen magance shi ba.

https://p.dw.com/p/1GBQz
Burundi Proteste Straßenbarrikade
Hoto: Reuters/G. Tomasevic

Wakili na musamman da majalisar ta tura yankin Abdoulaye Bathily shi ne ya ambata hakan bayan da ya kammala wata ganawa da shugaban kasar Rwanda Paul Kagame.

Mr. Bathily ya ce dole kasashen duniya su tashi tsaye wajen ganin an kawo karshen hatsaniyar da ta daibaiye kasar ta Burundi muddin dai ana son ganin zaman lafiya ya wanzu a tsakiyar Afirka.

Wakilin na Majalisar Dinkin Duniya ya ce lokaci ya yi da ya kamata al'ummar Burundi su amfana da zaman lafiya, inda ya kara da cewar yanzu ba lokaci ne na kashe-kashe ko ramuwar gayya ba, lokaci ne da za a fuskanci zaman lafiya mai dorewa.