1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Fargabar karuwar jam'iyyun kishin kasa

Lateefa Mustapha Ja'afar
February 27, 2017

Sakatare janar na Majalisar Dikin Duniya António Guterres ya yi gargadin cewa karuwar jam'iyyun 'yan rajin kishin kasa a duniya na yin barazana ga 'yancin dan Adam.

https://p.dw.com/p/2YJuM
Sakatare janar na Majalisar Dikin Duniya António Guterres
Sakatare janar na Majalisar Dikin Duniya António GuterresHoto: Reuters/D. Balibouse

Guterres ya yi wannan gargadin ne a yayin bude taro na mako hudu kan 'yancin dan Adam a Geneva. Ya kara da cewa masu tsananin ra'ayin kyamar baki da sunan kishin kasa da kuma masu tsastsauran ra'ayi na yin aiki kafada da kafada, ta hanyar karfafa tsana ga Musulmi da Yahudawa da wariyar launin fata da ma sauran nau'o'i na kabilanci da kyama a duniya baki daya. Ya nunar da cewa ya zamo tilas Hukumar Kare Hakkin dan Adam ta majalisar ta kasance sahun gaba wajen yaki da wannan dabi'a, koda yake ana zargin hukumar da amince wa da kasashen da ke sahun gaba wajen take hakkin dan Adam irin su China da Saudiya a matsayin mambobinta.