1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Fargabar kasa cimma muradin makamashi.

Gazali Abdou Tasawa
April 3, 2017

Bankin Duniya ya bayyana fargabar yiwuwar kasa cimma muradin da duniya ta sanya a gabanata na samar da makamashin lantarki ga ko wani dan Adam nan zuwa shekara ta 2030.

https://p.dw.com/p/2aXDN
Symbolbild Idee Strom Glühbirne
Hoto: colourbox/K. T. Segundo

Bankin Duniya ya bayyana fargabarsa a game da yiwuwar kasa cimma muradin da duniya ta sanya a gabanata na samar da makamashin lantarki ga ko wani dan Adam da kuma bunkasa hanyoyin samar da tsaftaccen makamashi nan zuwa shekara ta 2030. Bankin Duniyar ya bayyana hakan ne a cikin wani rahoto da ya wallafa a wannan Litinin. 

A cikin wata sanarwa da ta fitar kan wannan batu, wakiliyar sashen kula da harakokin makamashi a Majalisar Dinkin Duniya Rachel Kyte ta gargadi shugabannin kasashen duniya da su kara azama wajen saka wadatattun kudade a fannin samar da makamashi domin ganin an cimma wannan buri nan zuwa shekara ta 2030. 

Rahoton Bankin Duniyar ya ce a shekara ta 2014 akwai sauran mutane sama da miliyan dubu dari da ba su mallaki makamashi ba a duniya baki daya. Sai dai rahoton ya ce an samu ci gaba a fannin sama da makamashin a wasu kasashe kamar Afganistan, Kambodiya, Kenya, Uganda da Ruwanda.