1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Fargabar yiwuwar ɓillar rikicin ƙabilanci a Guinea

July 9, 2010

Ana shirin shiga zagaye na biyu don fid da gwani a zaɓen shugaban ƙasa a ƙasar Guinea nan da ƙarshen wannan wata

https://p.dw.com/p/OFTz
Shirye-shiryen zaɓe zagaye na biyu a ƙasar GuineaHoto: AP

A yau zamu fara ne da ya da zango a ƙasar Guinea, wadda bisa ga ra'ayin jaridar Neues Deutschland take ciki hali na zaman ɗarɗar dangane da yiwuwar ɓillar rigingimu na ƙabilanci bayan zaɓen ƙasar da aka gudanar baya-bayan nan. Jaridar ta ce:

"A zaɓen demoƙraɗiyya na farko da aka gudanar a ƙasar Guinea shekaru hamsin bayan samun 'yancin kanta wakilan manyan ƙabilu biyu na ƙasar ne suka samu rinjaye, amma kuma wajibi ne nan da makonni biyu masu zuwa manyan 'yan takarar su sake shiga zaɓen fid da gwani. A zagayen farko dai tsofon piraminista Cello Dalein Diallo ya tashi da kashi 39 da rara cikin ɗari, a yayinda Alpha Conde ya samu kashi 20 cikin ɗari sai kuma kashi 15 cikin ɗari na jumullar ƙuri'un da aka kaɗa ga Sidya Tuore. A dai ranar lahadi da ta wuce Tuore ya ce bai tsayar da shawara ba a game da wanda zai ba wa goyan baya. Sai dai kuma babbar matsalar dake akwai ita ce ta saɓanin ƙabilanci, inda ake iƙirarin cewar babakeren Fulani dake da rinjaye a ƙasar ka iya zama barazana ga haɗin kan al'umarta. Amma a haƙiƙanin gaskiya gwagwarmayar kama madafun ikon tana da nasaba ne da ɗimbim albarkatun da Allah Ya fuwace wa wannan ƙasa."

Ƙasar Kenya na fuskantar barazanar faɗawa cikin wani rikici na mulki, sakamakon ƙarin kuɗaɗen shiga da 'yan majalisar dokokin ƙasar suka yi wa kansu da kansu, kamar yadda jaridar Die Tageszeitung ta rawaito ta kuma ƙara da cewar:

Hunger / Ernährung / Afrika / Kenia / FAO / Welternährungsgipfel
'Yan majalisar ƙasar Kenya sun yi wa kansu ƙarin albashi a yayinda talakawan kasa ke cikin wahalaHoto: AP

"Majalisar dokokin Kenya dai tun da daɗewa tayi ƙaurin suna a game da facaka da dukiyar ƙasa. Amma a wannan karon wakilan majalisar sun nemi wuce gona da iri kamar yadda akasarin al'umar Kenya da suka gundura da al'amuran siyasar ƙasar ke gani. Domin kuwa a sakamakon matsin lamba akan biyan haraji daga albashinsu 'yan majalisar suka tsayar da shawarar yi wa kansu ƙarin albashi daga kwatankwacin Euro dubu takwas zuwa kusan Euro dubu 12 a wata. Idan an kwatanta da sauran sassa na duniya, inda misali a nan Jamus ɗan majalisa ke da albashin Euro dubu bakwai za a ga lalle kan wakilan na Kenya sun wuce makaɗi da rawa, kamar yadda jaridun ƙasar suka nunar."

Jaridar ta Neues Deutschland har ila yau ta leƙa Somaliya ta Arewa domin duba halin da ake ciki na zama lafiya da kwanciyar hankali. Jaridar ta ce:

Somaliland Hargeisa Skyline
Yankin Somaliland na da zaman lafiya amma ba a yi amanna da ƙasar baHoto: DW/Richard Lough

"A yayinda a ƙasar Somaliya ake fama da bata kashi ba ƙaƙƙautawa, amma a ɗaya ƙasar ta Somaliland al'amura na tafiya salin-alin ba wata matsala kuma daga baya-bayan nan ta naɗa sabon shugaban ƙasa sakamakon sahihin zaɓe na demoƙraɗiyya. Sai dai kuma kawo yanzu babu wata ƙasa ta duniyar nan da ta amince da haƙƙin wanzuwarta, lamarin da ya sanya ba ta samun wani tallafi daga bankin duniya ko ƙasashe masu ba da lamuni ta dogara ne kacokam da kanta. Ana kuma kyautata cewar yankin na da ɗimbin albarkatun ƙasa, musamman Uranium da Man Fetir, amma an kasa gabatar da ayyukan haƙansu duk da kwanciyar hankalin da Somaliland ke da shi kama daga shekara ta 1991."

Mawallafi: Ahmad Tijani Lawal

Edita: Umaru Aliyu