1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Fasahar Tagwaita Irin Shuka

June 23, 2004

A jiya talata ne aka fara taron nazarin matakan aiwatar da fasahar tagwaita irin shuka a nahiyar Afurka. Taron, wanda kamfanonin Amurka ke daukar nauyinsa, ana gudanar da shi ne a Wagadu, fadar mulkin kasar Burkina Faso

https://p.dw.com/p/Bvil
Manoma a Burkina Faso
Manoma a Burkina FasoHoto: Arsenijevic

An dai saurara daga bakin shugaban kasar Amurka George W. Bush yana mai yin nuni da muhimmancin wannan fasaha tagwaita amfanin noma domin shawo kan matsalolin Afurka. A lokacin da yake bayani game da haka shugaban na Amurka cewa yayi:

Kusan a kullu-yaumin sai mu nakalci fa’idar dake tattare da fasahar aiwatar da kwayar halittu a kasarmu. Kuma a yanzu wajibi ne a gabatarwa da kasashen Afurka masu tasowa, wannan fasaha domin su ci gajiyarta. Kasashe da dama na nahiyar Turai sun hana shigowa da hatsin da aka tagwata hallitarsu zuwa kasashensu, kuma a sakamakon haka kasashe da dama na Afurka ke kyamar kashe kudi akan wannan fasaha. Amma fa wajibi ne akanmu mu ba da kakkarfan taimako ga yaduwar fasahar tagwaita irin shuka ta yadda kwalliya zata mayar da kudin sabulu ga fafutukar yaki da matsalar yunwa a duniya baki daya.

To sai dai kuma duk da muhimmancin manufar ta yaki da matsalar yunwa, amma fafutukar ta shugaban kasar Amurka tana da alaka ne da wata manufar dabam. Manufar kuwa ita ce ta mara wa kamfanin Amurka na Monsanto baya, wanda shi ne kadai yake da ikon noman auduga ta amfani da irin shuka na BT da aka tagwaita kwayarsa a kasar Burkina Faso. An saurara daga ministan noma na kasar ta Burkina Faso Salif Diallo yana mai gargadin cewar zai zama babban kuskure idan kasashen Afurka suka yi fatali da fasahar tagwaita irin shuka saboda wannan fasahar ta taimaka kasarsa ke da ikon ribanya yawan audugan da take nomawa har sau hudu. Amma fa makobciyar kasa ta Benin ba ta da irin wannan ra’ayi, kamar yadda aka ji daga Didier Hubert Madafime daga ma’aikatar noma ta kasar, lokacin da yake yin nuni da yadda kamfanonin Amurka na Monsanto da Cognita ke kokarin yada angizonsu a sassa dabam-dabam na Afurka. Shawarar da kasar ta dauka shi ne a bata damar sararawa ta tsawon shekaru biyar har sai ta kammala binciken amfani da kuma rashin amfanin dake tattare da wannan fasaha, musamman ma wajen aiwatar da shinkafa da masarar da aka noma daga gareta. Wadannan kamfanoni na Amurka su kan shirya ire-iren wadannan tarurruka ne domin janyo hankalin kasashen Afurka dake adawa da fasahar su ba da kai bori ya hau ta kwadaita musu kazamar ribar da zasu iya samu daga gareta. Amma a hakikanin gaskiya wadannan kamfanoni sune wuka su ne nama. Saboda daga wajen su ne za a sayo irin shukan da ake bukata da kuma maganin kashe kwarin da ya dace da su. Kawo yanzun dai hakansu bai cimma ruwa ba, domin kuwa kasashen nahiyar sun ki amincewa da gwada fasahar a gonakinsu. A shekarar da ta wuce ma sai da aka shiga takun-saka tsakanin Zambia da Amurka, saboda kasar ta Zambiya ta ki karbar taimakon masarar da aka tagwaita irin shukanta daga kasar ta Amurka, inda ta gwammace da ta kwana da yunwa akan karbar wannan taimako.