1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Fashin jiragen ruwa a gabacin Afurka

June 27, 2007

Matsalar fashin jiragen ruwa ta zama ruwan dare, musamman a gabar tekun kasar Somaliya

https://p.dw.com/p/BtvD

Somaliya dai kasar ce da ta cancanci a lakaba mata taken yamutsi da rashin sanin tabbas, ganin irin halin da ta dade tana fama da shi na tashe-tashen hankula da tabarbarewar tsaro da rudami da kuma gwamnatoci na wucin gadi da basu da iyaka. Da kyar za a yini a kasar ba tare da an fuskanci musayar wuta ko fashe-fashen bamabamai ko harbe-harben kan mai uwa dawabi ba. A baya ga wannan mawuyacin hali sai ga shi ana fuskantar wani sabon yanayi na farfadowar ta’addancin ‘yan fashi n jiragen ruwa a gabar tekun kasar ta Somaliya. Pottengal Makundan shugaban hukumar sufurin jiragen ruwa ta kasa da kasa ya ce a halin da ake ciki yanzu haka tekun bahar-maliya ita ce tafi kowace hadari a duk fadin duniya. Akalla an kame jiragen ruwa da yawansu zai kai rabin dozin inda aka yi garkuwa da ma’aikatansu tun abin da ya kama daga farkon wannan shekara. Tun kimanin makonni da dama da suka wuce ‘yan fashin ke garkuwa da wani jirgin ruwan kamun kifi daga kasar Taiwan da kuma wasu jiragen ruwan jaura guda biyu na kasar Tanzaniya da kuma wani guda daya daga kasar Denemark. Wani jirgin ruwan na kungiyar taimakon abinci ta MDD dake dauke da tan dubu daya da dari takwas na kayan abinci, sai da yayi kwanaki 40 a hannun ‘yan fashin, kuma da kyar jirgin ya tsallake rijiya da baya wajen sake fadawa hannun ‘yan fashin karo na biyu. Pottengal Mukundan yayi imanin cewar haulakan yakin Somaliya dake da tasiri a gwamnati na da hannu dumu-dumu a matzsalar fashe-fashen jiragen ruwan. Mukundan ya kara da cewar:

“A saboda kasancewar ba a da wata tsayayyar gwamnati da hanyoyin sadarwa kuma babu doka da oda ya sanya ‘yan fashin ke cin karensu babu babbaka.”

Tun da ake yankin gabar tekun gabacin Afurka bai taba shiga wani mummunan hali na tsaro kamar yadda lamarin yake a yanzun ba. Jan Otte kaftin din rundunar ruwan Jamus dake sintiri a tekun bahar maliya karkashin matakin yaki da ta’addanci na kasa da kasa da aka gabatar a shekara ta 2003 yayi nuni da cewar:

“Akwai wasu tsayayyun kungiyoyin dake da hannu a miyagun laifuka masu nasaba da fashe-fashen jiragen ruwa daidai da yadda lamarin yake dangane da ayyukan ta’addanci.”

To sai dai kuma wani abin lura a nan shi ne a shekarar da ta wuce lokacin da gamayyar kotunan musuluncin Somaliya take mulki ba a fuskanci fashin jirgin ruwa ba ko da sau daya ne a tsawon wannan shekara.