1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Fashin jirgin ruwa a tekun Somaliya

October 24, 2010

´Yan fashi a tekun Somaliya sun yi awan gaba da wani jirgin ruwa mallakar ƙasar Singapor

https://p.dw.com/p/PmPB
Fashin jirgin ruwa a tekun SomaliyaHoto: AP

'Yan fashin teku a Somaliya sun sace wani jirgin ruwan ɗaukar kaya mallakar ƙasar Girka, amma wanda wani kamfanin ƙasar Singapor ya yiwo hayar sa, a lokacin da ya ke yin jigila a kan tekun ƙasar Kenya. Jirgin ruwan, wanda ke ɗauka iskar Gas, kana ya ke ɗauke da ma'aikata 17, rahotanni su ka ce 'yan fashin jiragen ruwan sun yi awon gaba da shi ne a wani yankin da ke da tazarar kilomita 165 a tsakanin tashar tekun Mombasa na ƙasar Kenya da kuma Tsibirin Seychelles. Babu dai wani ƙarin bayani game da halin da matuƙin jirgin ruwa, wanda ɗan asalin ƙasar Jamus ne ya ke ciki, tare da wasu 'yan ƙasar Ukrain su biyu da kuma 'yan Philipines 14.  A yanzunnan da ake batu dai 'yan fashin jiragen ruwa  daga ƙasar Somaliya su na riƙe da jiragen da yawan su yakai 20, da kuma ma'aikata 400 da suke yin garkuwa da su domin neman kuɗaɗe masu yawa gabannin sakin su. Yin garkuwa da ma'aikata da kuma jiragen ruwa ya zama ruwan dare a tekun na Somaliya, inda manyan jiragen ruwa daga ƙasashen duniya daban daban ke bi, kasancewar yankin tekun ya haɗe tsakanin nahiyoyi daban daban.

Mawallafi: Saleh Umar Saleh

Edita: Yahouza Sadissou Madobi