1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Faspo ɗin jabu domin kissan jagorar Hamas

August 14, 2010

Haɗaɗdiyar Daular larabawa ta koka game da sakin ɗan leƙen asirin Isra'ilar da ake zargi da kissar jagorar Hamas

https://p.dw.com/p/Onqu
Uri BrodskyHoto: AP

Hukumomin ƙasar Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa sun bayyana damuwar su ga hukumomin Jamus bisa sakin wani ɗan leƙen asirin Isra'ilar da ake zargi da yin amfani da jabun fasgo, bayan danganta shi da kissar wani jagorar Hamas wanda ke yin gudun hijra a birnin Dubai na Haɗaɗɗiyar Daular Larabawar. A jiya Jumma'a ce dai wata kotun Jamus ta bayar da belin Uri Brodsky, har sai ta kammala tantance ko yana da hannu wajen yin jabun fasgo na Jamus da ake dangantawa da kissar.

Wani jami'in ma'aikatar kula da harkokin ƙetaren Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa AbdurRahim al-Awadhi ya ce abin damuwa ne sakin da aka yiwa Brodsky zuwa Isra'ila a dai dai lokacin da ake ci gaba da sauraren shari'ar da ake yi masa.

Wani kakakin masu gabatar da ƙara a birnin Cologne na nan Jamus ya ce ba wai lalle bane sai a Jamus za'a yiwa Brodsky shari'a, yana mai cewar, akwai ma yiwuwar kotun ta yi masa tara kawai. Haɗaɗɗiyar Daular Larabawar dai ta ce wasu mutanen da suka yi amfani da jabun fasgo na ƙasashen Jamus, Faransa, da  Ireland da kuma Australia ne suka shiga ƙasar, tare da bindige Mahmoud al-Mabhouh - jagorar Hamas a wani Hotel dake birnin Dubai.

Mawallafi : Saleh Umar Saleh

Edita : Abdullahi Tanko Bala