1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Fata ga yaran masu neman mafaka a Jamus

November 20, 2010

Kamfanonin Jamus sun bayyana bukatar ƙarin horar da matasa akan ayyuka

https://p.dw.com/p/QEAe

Ministocin cikin gida na jihohi 16 da gwamnatin Tarayyar Jamus sun ba da shawarwarin amincewa da barin yaran 'yan gudun hijiran da basu da takardun izinin zama, ko da kuwa iyayensu na fuskantar barazanar kora daga cikin ƙasar. A taron da su ka gudanar a birnin Hamburg, ministocin sun bukaci bawa irin waɗannan yaran da suka riga suka shiga makaranta, damar cigaba da karatunsu.

Ministan  cikin gida na Hamburg Heino Vahldieck yace  iyayen waɗannan yaran suna da damar ci gaba da zama, idan har yaransu ba su kai shekarun balaga ba. Kafin nan sun yi  iyayensu sun yi cuɗanya tare da sajewa cikin mutanen ƙasar.

Sai dai gamayyar ƙungiyoyin dake wakiltan 'yan gudun hijira, sun soki wannan tsarin, kan cewar wannan shine mafi kankanci mafita ga lamarin. Akwai Baƙi 'yan gudun hijira kimanin dubu 87 da basu da takardun izinin zaman ƙasa a nan Jamus. Kamfanonin ƙasar dai sun bayyana bukatar cigaba da horar da matasa akan ayyuka daban-daban domin kalubalantar ƙaruwan karancin ma'aikata ƙwararru.

Mawallafiya: Zainab Mohammed Abubakar

Edita   :   Yahuza sadissou Madobi