1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Fata kan zaben Burkina Faso

Katrin Gänsler/Abdourrahmane Hassane/USUAugust 11, 2015

Nan da watannin biyu masu zuwa za'a gudanar da zaben shugaban kasa da na 'yan majalisun dokoki a kasar wanda shi ne zaben farko tun bayan kkawar da gwamnatin Blaise Compaoré

https://p.dw.com/p/1GDYZ
Burkina Faso Jubel nach dem Rücktritt des Präsidenten Compaore 31.10.2014
Hoto: AFP/Getty Images/I. Sanogo

Jama'a galibi dai matasa a kasar na cike da zumudin ganin an gudanar da zaben, domin wannan shine zai kasance na farko a kan tsarin dimokradiyya nagartacce tun bayan faduwar gwamnatin Compaore a cikin watan Oktoban bara.

Prosper Simpore, wani mai fafatuka wanda ya saka ido a juyin-juya halin da aka yi a Burkina Faso, ya jagoranci wata tawaga ta 'yan jaridu da wasu jami'ai na kasashen waje. Inda suka ziyarci gidan tsofin shugabannin mulkin na Burkina Faso musammun ma gidan Francois Compaore, kani ga tsohon shugaban kasar wato Blaise Compore. Mutumin da ya rike matsayin mashawarcin shugaban kasar kana daya daga cikin hamshakan attajirai na kasar, wanda ya rika sheke ayarsa kafin daga bisani gwamnatin ta fadi.

Gida nasa dai ya kasance kango ba kowa ciki har ma gara ta fara ci, kuma jami'an sun kai ziyara ne ana cikin yanayi na yin ruwan sama marka-marka.

''Prosper Simpore ke nan yana mai cewar zamu hau saman benin gidan, inda ke da dakunan 'ya'yan kanin tsohon shugaban kasa wato Francois Compaore, da kuma shi kansa ma, a nan akwai wurin wanka da wurin ninkaya da kuma sauran kayan alatu".

Hakika sabuwar dokar zabe da babbar kotun kolin kasar ta amince da ita, ta haramtawa tsofin shugabannin kasar sake tsayawa takara a zaben wanda bisa ga dukkan alamun Comporen da shi da danginsa, ba za su iya sake dawowa ba a kasar.

Yanzu haka dai ya rage watannin biyu kacal a gudanar da zaben shugaban kasar, wanda a kansa 'yan takara 11 za su fafata, kuma wasu jama'ar kasar na fatan ganin an kai ga yin zagaye na biyu a zaben shugaban kasar. Sai dai Sanu Aly babban magatakarda na kungiyar kare hakkin bil Adama ta kasar Burkina Faso, wato MBDHP ya ce jama'a su fitar da fargaba kan sake komawar tsofin shugabannin kan mulki.

"Ya ce Koma mi ake ciki yakamata a bar kowa ya halarci zaben, Blaise ba shi ne kan mulki ba, don haka ba shi ke kula da zabe ba. Ya ce kuma da dama daga cikin wasu na kusansa sun yi batan dabo. Galibi ma masu bada kudi ga jam'iyyarsa ni ina ganin mu yarda da al'umma tunda sune suka fito suka kori Balise daga mulki".

Ko da shi ke za a yi cewar kadaran kadahan, a cikin shekaru goma kasar ta Burkina Faso ta samu ci gaba, amma kuma ta kasance kasa mafi fama da juyin mulki a nahiyar Afrika. Tun daga shekaru 1983 a juyin mulkin da Compaore ya yi wa mutumin dake da kwarjinin jama'ar kasar, shekaru uku kawai bayan ya zo kan karagar mulki a karkashin jagorancin rundunar da ke tsaron fadar shugaban kasar.

Kuma har yanzu rundunar tsaron fadar shugaban kasar ta Burkina Faso na fada a ji a cikin harkokin mulkin. Domin ko a kwanan baya sun yi yunkurin ganin firaminista , Isaac Zida, ya yi murabus amma kuma ba tare a cimma nasara ba. Adama Ouédraogo wani dan jarida ya ce har yazuwa yanzu da sauran rina a kaba.

Ya ce " 'Yan siyasarmu da ke daukar kansu a matsayin 'yan demokaradiyya har yanzu ba su da kwarewa a wanan fanni, domin cikakken dan siyasa shi ne wanda zai yardda cewar ya fadi ya kuma amince da shan kaye. Ya ce a yanzu ba za ni iya tabbatar muku ba da cewar dukkanin wadanda za su halarci zaben za su amince sun sha kaye, idan mar har haka ta faru. Ya ce babban aikin da ya wajaba a kan kungiyoyin farar hula shi ne na kaucewa nuna zabi ko nuna son rai, abinda ke da mahimmanci shi ne dorewar zaman lafiya da harkoki a cikin kasa".

Manazarta dai a kasar ta Burkina Faso na korafin cewar daga cikin 'yan takara 11 wadanda za su tsaya takara a zaben, babu wani wanda ke da tsayayen tsarin fitar da kasar daga cikin halin da ta samu kanta a ciki, na talauci da sauran kalubale na rayuwa.

Burkina Faso Präsident Thomas Sankara
Marigayi Thomas SankaraHoto: picture-alliance/dpa
Burkina Faso Ex-Präsident Compaore Archiv 2011
Hambararren shugaba Blaise CompaoreHoto: picture alliance/AP Photo/R. Blackwell