1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Fatan mallakar mota a Najeriya na dishewa

January 12, 2017

Farashin motoci dai da ke cikin Najeriya ya yi tashin goron zabi abin da ke sa masu karamin karfi rasa karfin gwiwar iya sayen motocin don yin aiyyukansu na yau da kullum.

https://p.dw.com/p/2VhJW
DW Karikatur Nigeria Autos
Hoto: DW/A. Baba Aminu

Bayan da gwamnatin Najeriya ta aiyana hana shigo da motoci a kasar daga wasu kasashe ta iyaka ta kasa sai dai a shigo da su ta tashoshin jiragen ruwa na kasar, matakin da majalisar dattawan kasar ta yi fatali da shi, yanzu haka dai lamarin ya shafi masu hada-hada a wannan fanni musamman kasashe da ke makwabtaka da Najeriyar , alal misali masu wannan safara a Nijar makwabciyar Najeriya haka wadanda ke siyo motoci daga Jamhuriyar Bene kukan sike inda tuni wasu 'yan kasar Lebonon da ke kasuwancin motocin suka fara tattara ina su su ke ficewa daga kasar.

Deutschland Ahrensburg Fahrzeuge gebraucht Händler mit Kunden
Motocin ana dauko su daga kasashen duniyaHoto: Imago/Hoch Zwei/Angerer

A gidan ma dai ba ta sauya zani ba, inda dubban daruruwa na masu cin abinci a wannan fanni ke kokawa da hana musu hanyar cin abinci, baya ga wadanda  motocinsu ke bisa hanya dokar da aka tsara ta fara aiki a daya ga watan Janairun nan ta ritsa da su.

Matasan Benin na iya shiga rudani a cewar wani matashi Buhari a Jamhuriyar Bene inda dubban daruruwansu su ke dogaro, kasancewar an fara rufe manyan gareji na motoci saboda matsalar rufe iyakar ta Najeriya.

Bincike dai ya nuna cewa otel-otel na masaukin baki dake mu'amalla da motoci a yanzu duka an rufe su sabili da rashin masu shigowa cikin Birnin na Kwatono .

To sai dai a ranar Laraba majalisar dattawa ta Najeriya tayi fatali da matakin dagwamnati ta dauka kan haramta shigar motocin ta kasa.