1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

030310 Terroristen Fatwa

March 5, 2010

Ayyukan tarzoma ba su da matsayi a cikin addinin musulunci

https://p.dw.com/p/MKaX
Hoto: AP/IntelCenter

Babban malamin addinin musulunci kuma mai faɗa a ji Muhammad Tahir ul-Qadri ya nunar da cewa ayyukan tarzoma ba su da matsayi a cikin musulunci. A cikin Fatwar da ya bayar a birnin London, Tahir ul-Qadri shugaban ƙungiyar ´yan Sunna ta Minhaj ul-Qur´an daga ƙasar Pakistan, ya ce duk wani ɗan harin ƙunar baƙin wake ɗan wuta ne.

Dukkan ayyukan tarzoma ba su da tushe a cikin addinin musulunci, babu wata hujja ko dalilin aikata wannan ta´asa, inji Muhammad Tahir ul-Qadri mai shekaru 59 ɗan asalin ƙasar Pakistan kuma shugaban ƙungiyar ´yan sunni ta Minhaj ul-Qur´an kuma ɗaya daga cikin manyan malaman musulunci a Birtaniya. Tahir ul-Qadri wanda ya ba da wannan Fatwa a birnin London ya yi fatan cewa da wannan Fatwa zai kare matasa daga shiga hannun ƙungiyoyi masu matsanancin ra´ayi.

Tashe tashen hankula a Pakistan da ƙaruwar tsauraran ra´ayoyi tsakanin Musulmai a jami´o´in Birtaniya na daga cikin dalilan da suka sa ul-Qadri yin wannan Fatwa yana mai yin nuni da masu aikata tarzoma da sunan addinin musulunci. Ul-Qadri ya ba da hujjojinsa da ayoyi daga al-Qur´ani mai tsarki a cikin wata ƙasida mai shafuka 600. Ya ci-gaba da cewa duk mai aikata tarzoma ko ƙunar baƙin wake kahufri ne wanda wutar jahanna ce makomarsa. Ya ce bai kamata a danganta kalmomin kamar shahidai da jihadi da ayyukan tarzoma ba.

"Ina mai suka da kakkausan lafazi ga dukkan tsauraran ra´ayoyi da kuma dukkan ayyuka na tarzoma da ake aikatawa da sunan addinin musulunci bisa mummunar fahimta ko fassarar da wasu ke yiwa addinin."

Wannan Fatwa dai ta ɗan janyo kace-nace a ciki da wajen Birtaniya musamman tsakanin wasu malaman addinin musulunci da kawo yanzu ba su fito ƙarara suka nesanta kansu daga ayyukan tarzoma ba. Ko da yake wannan Fatwar ta ul-Qadri ita ce mafi girma amma ba ita ce kiran farko ta wannan ɓangaren ba. Domin bayan hare haren da aka kai a London a shekarar 2005, manyan limamai a Birtaniya sun yi kakkausar suka ga ayyukan tarzoma. Su ma musulmai a wasu ƙasashen Turai ciki har da nan Jamus da duniya musulmi sun fid da Fatwa makamanciyar wannan.

Alal misali malaman addinin musulunci na kurkusa da gidan sarautar Saudiya su ma sun yi suka ga ayyukan tarzoma kana sun gabatar da wani shirin tallafawa masu yin watsi da tarzoma ta addini.

To sai dai duk da waɗannan kiraye-kirayen da suka da ma Fatwa ba za su sa a daina ayyukan ta´addanci na addini ba. Hatta ma wannan sabuwar Fatwar ba za ta kawo ƙarshen su ba. Ko da yake Fatwa wajibi ce a addinance amma babu wasu ƙa´idoji a bayyane da suka fayyace wanda ko kuma irin Fatwar da ya kamata a yi aiki da ita.

Mawallafa:Peter Philipp/Mohammad Nasiru Awal

Edita: Ahmed Tijani Lawal