1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Fidel Castro na fama da rashin lahia.

Yahouza Sadissou MadobiAugust 1, 2006

Shugaban Cuba Fidel Castro ya danƙa mulkin wucin gadi a sakamakon rashin lahia da ya ke fama da ita.

https://p.dw.com/p/Btyo
Hoto: AP

Shugaba Fidel castro na ƙasar Cuba na cikin wani hali na mutu kwakwai rai kwakwai, bayan aikin teyata ko kuma fashi da likitoci su ka yi masa, a sakamakon matsananciyar rashin lahia.

Sanarwar da shugaban ya sa ma hannu, kuma sakataran sa na mussamman Carlos Manuel Valengia ya karanta wa kafofin sadarwa,ta bayana cewar:

Aikin teyata da a ka yi mani ,na buƙatar in samu hutu na tsawan yan makwani, nesa da riginginmun harakokin mulki.

Ta la´akari da halin barazanar da ƙasar mu ke fuskanta daga Amurika, na yanke shawarwari kamar haka:

Na farko, na danƙa mulkin wucin gadi na sakataran zartsawa na jami´iyar Communisanci ta ƙasa ga Raul Castro Ruz.

Na 2, na danƙa matsayin shugaban rundunar tsaro ta ƙasa ga Raul Castro Ruz.

Na kuma danƙa a matsayin wucin gadi matsayi na shugaban kasa ga mataimaki na Raul Castro Ruz.

Sanarwar mai kama da wasiya, ta yi bitar gwagwarmaya da shugaban ya sha fama da ita,wajen ƙwatar yancin Cuba daga Amurikawa.

Sannan ta yi kira ga al´umomin Cuba, da su haɗa kai domin ci gaba da kare daraja da martarbar ƙasar.

Fidel Castro ya buƙaci su bada haɗin kai, ga taron shugabanin ƙasashe masu tasowa, da za a shirya a birnin Lahavane a cikin watan Satumber mai zuwa , taron da bisa dukan alamu ba za shi halartar ba.

A dangane da bikin zagayawar shekaru 80 da aihuwar sa, da za a shirya ranar 13 ga watan da mu ke ciki, Castro ya bukaci a ɗage wannan shagulgulla har zuwa watan Desember.

A ƙarshe sanarwar ta gayyaci sojoji da komitin zartaswa na jam´iya da su bada haɗin kai ,ga dukan batutuwa da sanarwar ta ƙunsa.

Wannan shine karo na farko ,tun shekaru 47 da ya hau karagar mulki Fidel Castro ya bada karagar mulkin wucin gadi .

Raul Castro mai shekaru 65 a dunia ,da zai ɗauki yaunin jagorancin ƙasar na matsayin ƙane, kuma mataimakin shugaban kasa,bugu da ƙari ministan tsaro.

A halin da ake ciki titina a birnin Lahavane tsit, ka ke ji inda wasu ma, ke bayyana cewar shugaban ya riga mu gidan gaskiya.

A nasu ɓangare, yan adawar Kuba da ke gudun hijira a ƙasar Amurika, sun shirya liyafa a sakamakon wannan sanarwar, da ta su ka yi lale marhabin da ita.

Shugaban Fidel Castro, ya kasance shugaban ƙasar da ya fi daɗewa kan karagar mulki adunia.

Ya yi fama da gwagwarmaya da shugabani 10, na Amurika, a Amurrika, amma sun buga sun barshi.