1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Filipins ta soke hukuncin kisa a cikin kasar

June 24, 2006
https://p.dw.com/p/Busm

Kwana daya gabanin ta fara ziyara a fadar Vatikan, shugabar Filipins Gloria Arroyo ta sanya hannu kan wata doka da zata haramta zartas da hukunci kisa a cikin kasar. Tun kimanin makonni biyu da rabi da suka wuce majalisar dokokin kasar ta amince da kafa doka duk da kin haka da dangin wadanda ayyukan tarzoma ya shafa suka yi. A cikin shekara ta 1993 kasar ta sake maido da hukuncin kisa, amma hakan ya sha suka dakakkusar harshe daga majami´ar katholika mai fada a ji a kasar da kuma KTT da sauran kungiyoyin kare hakkin bil Adama. Daga wannan lokaci zuwa shekara ta 2000 an aiwatar da hukuncin kisa akan mutane 7 a kasar ta Filipins. Yanzu haka dai za´a mayar da hukuncin kisan da aka yankewa mutane kimanin dubu daya da 200 zuwa hukuncin daurin rai da rai a gidan kurkuku.