1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Fillon ya zama dan takarar adawa a Faransa

November 28, 2016

Francois Fillon mai ra'ayin mazan jiya ya yi nasara a zaben da zai bashi dama ta takarar shugabanci a Faransa, a daidai lokacin da masu kin jinin baki ke samun magoya baya.

https://p.dw.com/p/2TLYA
Frankreich Francois Fillon Ex-Premier
Hoto: Reuters/G. Fuentes

Francois Fillon ya yi nasara a matsayin wanda aka zaba ya yi takarar neman shugabancin kasa daga bangaren jam'iyyar masu ra'ayin mazan jiya ta 'yan Republican a Faransa, abin da zai bashi dama ta bude babi a fafutikar neman makoma ga Faransa, ya tunkari kalubalen makomar kasar a Kungiyar Tarayyar Turai ta EU da ma siyasa da sauran kasashen Yamma da duniya.

Bayan dai zaben Shugaban Amirka da Donald Trump ya lashe, zaben Faransa a watan Afrilu da Mayu mai zuwa na zama manuniya kan irin karfi da 'yan kishin kasa masu akidar yaki da masu tsatstsauran kishi na addinin Islama ke samu ko akasin haka a duniya.

Magoya bayan Fillon dai na ganin fafutikarsa ta kare al'adun Faransa da yaki da masu tsatstsauran kishin addinin Islama da yaki da masu aikata laifuka za su taimaka masa ya fiskanci 'yan jam'iyyar su Le Pen a zabe na gaba.