1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Fina-finan Hausa a Nijer da Najeriya

August 13, 2009

Ziyarar shugabannin hukumar tace fina-finan Hausa ta Kano zuwa Maraɗi a Nijer

https://p.dw.com/p/J8x9

A kwanakin baya tawagar hukumar tace fina-finan Hausa ta Kano a Najeriya ta kai ziyara a jihar Maraɗi ta Janhriyar Nijer domin sada zumunci da kuma ƙarfafa dangantaka tsakaninta da masu shirya fina-finan Hausa na Nijer. Wannan ziyarar ta zo ne a daidai lokacin da fina-finan Hausa ke daɗa samun bunƙasa a Janhuriyar ta Nijer baki ɗaya. Tawagar ta gana da sarakunan gargajiya da na zamani da kuma waɗanda ke da hannu a harkar shirya fina-finan Hausa a Maraɗi.

Mawallafi: Mohammad Nasiru Awal

Edita: Yahouza Sadisou Madobi