1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Finnland ta karbi shugabancin bayayya na kungiyar EU

July 1, 2006
https://p.dw.com/p/Bus9

Daga yau asabar daya ga watan yuli, kasar Finnland ta karbi shugabancin karba karba na KTT na wa´adin watanni 6 masu zuwa. Kasar ta maye gurbin Austria kuma zata kasance mai jan ragamar majalisar zartaswar kungiyar ta EU. FM Finnland Matti Vanhanen ya ce daya daga cikin muhimman batutuwa dake gaban su shi ne tattaunawar daukar Turkiya cikin kungiyar. Ana fuskantar matsaloli a wannan tattaunawar saboda kin da Turkiya ta yi na amincewa da tsibirin Cyprus. Acikin watan oktoba ake sa ran samun wani rahoto akan wannan batu. Vanhanen ya ce zai matsa kaimi wajen ganin EU ta kara kasafin kudi ga aikin bincike, raya kasa da kuma karfafa huldodi da Rasha musamman a fannin makashi. Jamus zata karbi shugabancin EU daga hannun Finnland farkon watan janerun badi idan Allah Ya kaimu.