1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Firamiyan ƙasar Sin zai fara wata ziyara a nahiyar Afirka.

June 14, 2006
https://p.dw.com/p/Buu8

Firamiyanm ƙasar Sin, Wen Jiabao, zai fara wata ziyarar mako ɗaya a nahiyar Afirka tun daga ran asabar mai zuwa. Wata sanarwar da gwamnatin ƙasar ta bayar a birnin Beijing, ta ce Firamiyan zai ziyarci ƙasashen Masar, da Ghana, da Jumhuriyar Kwango, da Afirka Ta Kudu da Angola, da Uganda da kuma Tanzaniya ne a cikin mako ɗayan.

Masharhanta dai na ganin cewa, Sin na ƙarfafa hulɗoɗin dangantaka na nahiyar ta Afirka ne saboda matuƙar bukatar albarkatun ƙasa da kuma makamashi da take yi. A halin yanzu dai, Sin na samun kusan kashi ɗaya bisa uku na man fetur da take bukata ne daga nahiyar Afirka.