1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Firamiyan Birtaniya Tony Blair ya fara rangadin ƙasashen Gabas Ta Tsakiya.

December 15, 2006
https://p.dw.com/p/BuXn

Firamiyan Birtaniya, Tony Blair, ya fara wani rangadin ƙasashen yankin Gabas Ta Tsakiya yau, tare da ya da zango a ƙasar Turkiyya. Ana kyautata zaton cewa, Tony Blair, zai ƙarfafa wa Turkawan gwiwa ne a fatar da suke yi na samun shiga cikin ƙungiyar Haɗin Kan Turai. Kazalika kuma, a nan zai fara shawarwarinsa, da ake gani kamar wani yunƙuri ne na farfaɗo da shawarwarin zaman lafiya a yankin Gabas Ta Tsakiya. Shi dai Blair, na cikin magoya bayan bukatar da Turkiyyan ke yi ta zamowa mambar ƙungiyar EUn, inda yake ganin za ta iya taka muhimmiyar rawar gani wajen ƙulla wata hulɗa ta musamman tsakanin ƙasashen Yamma da ƙasashen musulmi masu sassaucin ra’ayi.

Firamiyan na Birtaniya, wanda zai sauka daga muƙaminsa a shekara mai zuwa, ya sha kuma bayyana ra’ayin cewa, shawo kan rikicin Isra’ila da Falasɗinawa abin da zai iya janyo kwanciyar hankali a Iraqi da ma samad da zaman lafiya mai ɗorewa a yankin Gabas Ta Tsakiyan baki ɗaya.