1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Firamiyan Birtaniya Tony Blair ya gana da takwaran aikinsa na Isra’ila Ehud Olmert don yin shawarwari.

September 10, 2006
https://p.dw.com/p/Buk1

Firamiyan Birtaniya Tony Blair ya yi gana da takwaran aikinsa na Isra’ila Ehud Olmert a birnin Tel Aviv don tattauna batun farfaɗo da shawarwarin samad da zaman lafiya a Gabas Ta Tsakiya. Da yake jawabi a wani taron maneman labarai bayan ganawar, Ehud Olmert ya bayyana cewa a shirye yake ya sadu da shugaban Falasɗinawa Mahmoud Abbas ba da wani sharaɗi ba. A cikin nasa jawabin, Blair ya ce yarjejeniyar tsagaita wutar da aka cim ma a Lebanon ƙarƙashin laimar Majalisar Ɗinkin Duniya, za ta iya kasancewa, wata sabuwar hanya ta farfaɗo da shawarawrin daftarin nan na samad da zaman lafiya. A gobe ne dai ake sa ran Tony Blair zai tashi zuwa Lebanon, don yin shawarwari da Firamiyan ƙasar Fuad Siniora. A halin da ake ciki dai, wani jirgin ruwan Faransa ɗauke da dakaru ɗari 2, ya isa a tashar jirgin ruwan Beirut. Dakarun dai za su je kudancin Lebanon ne don shiga rundunar ƙasa da ƙasa ta kare zaman lafiya da Majalisar Ɗinkin Duniya za ta girke a yankin. Tuni dai jiragen ruwan yaƙin Faransa da na Italiya da kuma Girka na sintiri a gaɓar tekun Lebanon ɗin, don hana ’yan fasa ƙwauri kai wa ƙungiyar Hizbullahi makamai.