1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Fitaccen dan damben duniya Muhammad Ali ya rasu

Salissou BoukariJune 4, 2016

A ranar Juma'a ce Allah ya yi wa Muhammad Ali rasuwa yana dan shekaru 74 a duniya bayan ya yi fama da rashin lafiya da ke da nasaba da matsalar nunfashi.

https://p.dw.com/p/1J0Pi
USA Muhammad Ali Liston Knockout in Maine
Hoto: Neil Leifer

A ranar Alhamis ce dai da ta gabata aka kwantar da shi a wani asibiti da ke birnin Arizona na kasar ta Amirka bayan da cutar ta tsananta, kuma ya zuwa ranar ta Juma'a cutar ta kara tsananta a jikinsa, inda daga bisani rai ya yi halinsa.

Sunansa na ainihi dai shi ne Cassius Clay, amma ya koma Muhammad Ali bayan ya zama musulmi a shekarar 1964 shekarar da ya zama zakaran damben duniya. An haifi shi ne a ranar 17 ga watan Janairu na 1942 a birnin Louisville da ke kasar Amirka. Marigayin ya soma wasannin damben ne gadan-dagan tun daga shekarar 1960. kuma daga wannan shekara zuwa 1981 inda ya yi karawarsa ta karshe, Muhammad Ali ya yi karawa 61 kuma cikinsu ya samu nasarori sau 56.

Muhammad Ali ya samu karramawa ta zaman lafiya daga Majalisar Dinkin Duniya a shekarun 1998 da 2008 sannan ya samu wata karramawar ta zaman lafiya ta Otto Hahn a shekara ta 2005 da kuma babbar karramawa da ake iya baiwa wani farar hulla a kasar Amirka da aka kira Medal of Freedom a 2005. Muhammad Ali ya rasu ya na dan shekaru 74.