1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Fitar Birtaniya daga Tarayyar Turai

June 16, 2017

Makon mai zuwa kungiyar Tarayyar Turai za ta fara tattaunawar ficewar Birtaniya daga cikin kungiyar karkashin tattaunawa mai cike da sarkakiya.

https://p.dw.com/p/2emXI
Dokumentarfilm Ein Brexit und drei Millionen Sorgen
Hoto: WDR/dpa/Yui Mok

Kungiyar Tarayyar Turai da kasar Birtaniya a hukumance za su fara tattaunawa kan shirin fitar Birtaniya daga cikin kungiyar a ranar Litinin mai zuwa, da ke zama 19 ga wannan wata na Yuni, kamar yadda aka tsara. Michel Barnier ke zama babban jami'in Tarayyar Turai da zai jagoranci tattauna tare da David Davis ministan Birtaniya mai kula da fitar kasar daga cikin Tarayyar Turai.

Wannan yana zuwa bayan masu zabe a Birataniya sun kada kuri'ar da babu wata jam'iyya da ta samu nasara kai tsaye wajen kafa gwamnati ta gaba. Yanzu haka Firaminista Theresa May ta dogara da wata karamar jam'iyya mai kujeru 10 kacal a majalisar dokon mai mambobi 650, domin samun goyon baya kan duk wani kudiri a majalisar dokoki. Tattaunawar tsakanin Birtaniya da kungiyar Tarayyar Turai za ta dauki tsawon shekaru biyu, zuwa watan Maris na shekara ta 2019, saboda Birataniya ta fara amfani da ayar dokar ta ficewa daga Tarayyar Turai a watan Maris na wannan shekara ta 2017.

Abu na farko da bangarori za su bayar da fifiko a kai shi ne damar 'yan kasashen Turai da Birtaniya da ke bangarorin biyu, da harkokin kasuwanci da kuma tsaro.